Yanda Ake Yin Wankin Kai Da Karkashi Gashi Yayi Kyau Yayi Tsayi Da Baki Sannan Yayi Laushi:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Yau na kawo muku yanda ake yin amfani da Karkashi domin gyaran gashi.

Da akkwai hanyoyi da dama da Ake yin Wankin kai da karkashi, amma ga kadan daga cikinsu:

Da farko zaki samu busasshen karkashi ki dakashi aturmin qarfe sai kisa ruwa mai zafi a bap na wanka sai ki zuba karkashin dan dai-dai sannan ki zuba shampoo ki saka ruwan toka koh kanwa sai ki kada zakiga yayi kumpa sosai kuma yayi kore shar sannan ki tsaga tsakiyan kai ki raba gashi gida biyu sai kisa ki sunkuyo cikin bap din sai ki kulle gefe daya ki wanke dayan ruwa ya shiga sosai ki murza da kyau sai ki matseshi ki dauko cokali idan kika matse sai ki katse shi da cokali ruwan yana bin jikin cokali har sai kinga ya daina sannan ki daure shi sai kiyima dayan gefen shima haka, idan ya bushe kika taje kan zakiga idan da akwai abin karkashin zai fita sai ki samu mai oil koh man zaituun ki shafa shikenan.

Note: Abinda yasa ake saka ruwan toka aciki saboda idan kinada dandrupp ne zaifita.

Ga Hanya Ta Biyu:

Zaki samu busasshen karkashi ki jika idan ya jiku zakiga har kauri yake saiki kankare cocomber da Albasa kisa a ciki sannan in kina da lalli shima kisa saiki bari suma sudan jiku Koda na awa daya ne sannan ki wanke kai dashi.

Hanya Ta Uku:

Zaki zubama karkashin ruwan dumi kimurjeshi zakiga yana yauki sekisa shampo zaki iya tacewa kicire ganyan sekiraba gashinnan kamar zakisa mai seki rinka diban ruwan karkashin kina ciccudawa harsekin gama sannan ki taje kinayi kina matse ruwan idan ruwan yatsane sai ayimiki songas.

Hanya Ta Hudu:

Shima dai zaki jika karkashin da ruwan dumi dai-dai yanda zai isheki sai ki raba gashin biyu ki wanke rabi ki cuda harsai ruwan karkashin ya shiga sai kisaka shampo ki chuda sai ki saka ruwan karkashin ruwan ki wanke tas har kumfan ya fita, haka zakiyiwa daya part din shima.

Hanya Ta Biyar:

Zaki saka ruwanki kamar cikin karamar buta sai kizuba a robar wanka kisaka shampo da karkashin aciki yaikumfa saiki samutun ya sunkuyo kiwanke mai kidauraye da wani ruwan dan maikyau saiki tufke kishafa mai idan yabushe zakiga yayi kamar shampoo

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*