
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
Shin Menene Kawowa Wato (Inzali):
Inzali wato saurin zuwan kai wanda a turance ake kiran sa da Quick Ejaculation matsala ce babba, wacce take yawan damun akasarin maza a lokacin yin jima’i.
Amma ”duk mai fama da wannan matsalar in shaa Allahu idan aka daure aka hada wannan maganin za’a samu waraka da dacewa da izinin Allah.
Sannan kuma ba sai anje anata shan wasu kwayoyin bature ba, ga maganin da zan baku ku hada shi da kanku wanda in dai matsalar saurin zuwan kai/kawowane toh an wuce wurin da ikon Allah.
Ga Yanda Zaku Hada Maganin:
Abubuwan Buƙata Sune:
- Ganyen kargo mai dan yawa za’a samu.
- Lemun tsami guda 5 sai.
- Zuma mai kyau.
Yanda Za’a Hada:
Za’a wanke ganyen kargon sosai sannan a yayyanka lemun tsamin a zuba a turmi a hadasu waje daya a kirbasu, bayan an kirba sai a sauke a tafasasu su tafasa sosai, bayan sun tafasa sai a sauke a tace a zuba zuma babban cokali biyar idan ya dan huce sai asha yana da dadin sha kamar ana shan lemu.
Ana so a wannan wunin mutum ya mayar dashi ruwan shansa a kalla mutum ya sha kamar galan daya zuwa galan daya da rabi.
Dan uwa bazan maka rantsuwa ba amma in dai matsalar ka ta saurin kawowa ne toh in shaa Allahu ka wuce wajen saboda mutane da yawa sunyi Kuma sunji dadi don sunga amfanin yinshi.
Sannan kuma duk yanda kakai da rashin kokari wajen jima’i matukar ka yi wannan hadin toh kuwa zakaga canji fiye da yanda kake ada.
Mata Ga Naku Kuma Na Karin Ni’ima Baki Ba Korafin Miji:
Za’a samu ganyen gamji a shanya shi ya bushe sai a hada shi da garin dabino a saka madara ta ruwa koh ta gari a rinka sha kullum, toh in shaa Allah in dai Ni’ima ce matsalarki kema an wuce wajen.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply