
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
Ba kowani lokaci ne iyalai suke samun natsuwa ba matukar suka hadu koh suka fara ganin alamu na jini alhali suna da ciki.
Da akwai fitar jinin da bana matsala bane shine wanda yake fita a hankali tare da wasu ruwa wato sport haka wannan yana daya daga cikin alamomin implantation bleeding wanda nace ganin jini kasan-kadan a lokacin da mace take dauke da juna biyu Amma kasa da wata biyu ba matsala bace, saidai idan kuma an jawota ta zama matsalar daga baya.
Sannan ,mata Kashi 20% na mata han hadu da wannan alamar da ake kira da (Implantation Bleeding) Wanda kwata-kwata bashi da matsala, bashi daga cikin abinda ke zubar da ciki koh alama ta lalacewar ciki, da dama muna samun mata da wannan yanayin musamman ga matan da Basu zarce Wata biyu da samun cikin ba.
Tada hankali da matan kanyi musamman masu zumudin ciki koh wadanda suke da bukatan cikin ido rufe ke janyo musu wannan alamar ta zama matsala har ayi sanadiyar lalacewar cikin ta hanyar Anfani da wasu ababen da Kuma dena wasu ababen a gida, idan ma akai rashin sa’a toh a asibiti koh chemist za’a lalata cikin koh a zubar dashi ba gaira babu dalili wannan shi ake kira da garin Neman gira sai a rasa ido.
- Wannan jinin da ake gani yana faruwa ne sanadiyyar kyankyasasshen Kwan halittar mace Daya riga ya faru tsakanin sa da Sperm cells (kwayar halittar maniyyi) din Namiji kenan wanda daga karshe yayi Implantation din kansa cikin Mahaifar lokacin da yake wannan da Iznin Allah sai wannan jinin kadan-kadan gami da majina-majina su rinka fitawa mace, sai mace tarinka ganinsu zuwa wani lokaci.
Ku guji shan magungunan infection da sauran wasu magungunan da zasu lalata muku cikinku, a sanadiyyar alamar da hakan da kuka gani.
Ga wasu hanyoyin da zakuyi Amfani dasu a gida don magance wannan alamar a cikin sauki.
- Ki rinka samun wadataccen hutu.
- Amfani da Pads a maimakon tampons a gida ta yanda za’a samu dadewar hanyoyin da jinin sukan biyo.
- Amfani da mild pain relief kamar irinsu paracetamol kadai, matukar za ayi Amfani da kowanni maganin rage radadi toh lallai zai iya lalata Cikin sai a kiyaye.
- Sannan zuwa asibiti mafi kusa da zaran anga abinda ba’a gane mishi ba, da kuma kebentuwa da amfani da manyan magunguna na antibiotics da sunan mace nada infection.
- Gujewa uwar gida, ya zama wajibi maigida ya nade mayafinsa har aga abinda Allah zaiyi na tsayawar jinin, yin Jima’i a wannan lokacin yana daga cikin abinda yake zubar da cikin cikin sauki.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply