Amfanin Da Muhimmancin Kankana Tare Da ‘Ya’Yanta Ga Ma’aurata:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Hausawa suna yiwa kankana kirari da cewa, “Kankana uwar ruwa” wannan suna kuwa ya dace da ita, duba da yanda manazarta da ma su bincike suka tabbatar da cewa, fiye da kashi 90 cikin dari na kankana ruwa ne, sai dai, ba yawan ruwan ne yasa kankana tayi fice wajen yanda mutane ke mu’amala da ita ba, musamman a lokacin zafi, baya ga haka kankana na kunshe da wadansu sinadarai ma su yawan gaske dake da fa’ida wajen inganta lafiyar dan-adam.

Misali daga cikin amfanin da ake samu daga jikin kankana har da maganin ciwon olsa, maganin cushewar ciki dadai sauran su, na taba sauraron wata hira da wani gidan radio ya gudanar da wani babban likita a daya daga cikin asibitocin kasar nan, da aka tambaye shi game da amfanin kankana ga lafiyarmu, sai yace, dukkan jikin kankana babu na yarwa, kama daga kwallonta da kuma bawonta, saboda haka kamar yanda yace, dukkan ilahirin kankana na da amfani ga lafiyar jikin dan adam.

Misali binciken masana ya nuna cewa, Kwallon kankana na dauke da sinadaran proteins, vitamins, omega 3 and omega 6 fatty acids, magnesium, zinc, copper, potassium wadanda keda matukar amfani ga lafiyar Dan Adam.

  1. Yana Inganta Lafiyar Zuciya:

Kankana yanada matukar amfani wajen inganta lafiyar zuciyar mutum, musamman ma kwallonta, wanda ke dauke da sinadarin magnesium, da kuma ‘fatty acids’. Kamar yanda “American Heart Asociation” ta bayyana cikin wani bincike su wadannan sinadarai kare mutum daga Kamuwa da bugawar zuciya, da kuma rage kwalastaral na cikin jini dake yiwa mutum illah a lafiya.

  1. Yana Gyaran Fata:

Yawan cin kwallon kankana musamman idan an soya su, yanada amfani wajen gyaran fata, sannan kuma yana hana koh riga-kafin fitowar kurajen fata, ya na hana bushewar fata, da kuma dusashewarta, da kuma hana bayyanar alamun tsufan fatar mutum, toh wannan dalilin ne yasa yawan amfani da kwallon kankana kan taimakawa wajen hana yankwanewar fatar, kuma wannan yana daya daga cikin dalilan dayasa yakamata mutane su rinka cin kwallon kankana a kai a kai.

Bayan haka, yawan cin kwallon kankana don samun lafiyayyiyar fata mai sheki da laushi, hakanan masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa amfani da man kwallon kankana kan fata na kara inganta lafiyar fata ya hana fesowar kuraje da yamushewarta.

Sannan kuma ana amfani da bawon kankana wajen gyaran fuska ta yi kyau tayi gwanin ban sha’awa, ga mai son wannan fa’ida ta kankana sai ya rinka goga bawonta a fuskarsa, idan ya bushe sai ya wanke da ruwan dumi ya shafa man Zaituun, yin hakan nasa fuska tayi kyau cikin karamin lokaci.

  1. Ga Maza Kuma Yanasa Karfin mazakuta:

Kara dankon aure tsakanin ma’aurata, sakamakon kara karfin mazakutar namiji da zai samu damar gamsar da iyali, binciken zamani ya tabbatar da cewa Sinadarin ‘Arginine’ da ke kunshe cikin kankana na kara karfin maza kamar yadda magungunan kara karfi na zamani ke yi.

  1. Yana Taimakawa Masu Fama Da Hawan Jini:

Yawan shan kankana na matukar taimakawa mutanen dake fama da hawan jini wajen saukar sa, musamman ma kwallon kankana, kamar yanda na bayyana a sama kwallon daga cikin sinadaran da kwallon kankana ke kunshe da su akwai, ‘vitamins, niacin, folate, thiamine, vitamin B6 and pantothenic acid, wadannan sinadarai sun matukar taimakawa masu hawan jini ta hanyar inganta hanyoyin jini.

  1. Sannan kuma yana maganin kasala da samar da kuzari a Jiki:

Masana suna danganta yawan shan kankana da sanya kuzari a jiki, saboda haka shan kankana musamman tare da kwallonta na kara wa jiki kuzari fiyeda yanda ake tsammani.

Yanda mutum zaiyi amfani da kankana don samun karin kuzari kuwa shine, ya rinka matse ruwan kankanan yanasha, yin haka na kara kuzarin jiki sosai, bayan karama maza karfin mazakuta lokacin jima’i.

  1. Sannan yawan shan kankana yana sanya rauni koh wani ciwo da mutum ya ji ya warke cikin gaggawa.
  2. Yana Gyaran Gashi:

Sinadaran Protein, Iron, magnesium da copper na daga cikin muhimman sinadaran da ake iya kiransu abincin gashi, ita kuma kankana Allah ya hore mata wadannan sinadarai masu yawan gaske a cikinta, saboda haka ne yin amfani da kankana akai-akai kan inganta lafiyar gashinki, musamman ma ga matar da ke fama da zubewar gashi.

Kamar yanda binciken ya nuna, sinadarin ‘Protein’ na kara yawan gashi, shi kuma ‘magnesium’ yana hana zubewar gashi, a yayinda shi kuma sinadarin ‘Copper’ ke ƙara sheki da yalyalin gashi.

  1. Yana Saka Saurin Murmurewa Daga Lafiya:

A lokacin da mutum ya warke daga wata rashin lafiyar da yayi, idan ya juri amfani da kankana jikinsa zaiyi saurin farfadowa.

  1. Yawan Shan Kankana na taimaka wa mutum ya samu isasshen barci.
  2. Yana Kara Karfin Garkuwar Jiki:

Kamar yadda bincike ya nuna kankana na kunshe da sinadarin Bitamin C, wanda ke kara karfin garkuwar jiki, sakamakon haka sai kare jiki daga kamuwa daga cututtuka.

  1. Yana Karawa Mata Ni’ima A Lokacin Jima’i:

Kankana ta shahara wajen karawa mata ni’ima yayin saduwar aure, idan mace na fama da rashin ni’ima koh bushewar gaba, sai ta yi amfani da kankana don maganin wannan matsalar tata.

Yanda kankana ke karawa mata ni’ima shine, uwargida zaki samu kankana ki yanka ta sannan ki cire wallon ki samu dabino ki saka daga nan ki markada su, sai ki samu zumarki mai kyau mare hadi, ki zuba sannan ki hada da madara, sai ki adana kayanki cikin firij yayi sanyi ki sha, daga bisani sai ki samu kobawon kankanar ki shanya shi har sai ya bushe, bayan kin yi wanka sai ki turara farjinki da shi, wannan hadi na saurin karawa mace ni’ima sannan ya na kara ma ta sha’awa da kuma gamsar da mai-gida.

  1. Yawan shan kankana na kara inganta lafiyar Koda:
  2. Daga cikin amfanin kankana ga lafiyar dan adam, akwai kare mutum daga hadarin kamuwa da cutar ciwon daji.
  3. Yana Maganin Gyambon Ciki wato (Ulcer):

Kamar yanda na ambata a farkon wannan bayanine nawa, daga cikin amfanin kankana ga lafiyarmu har da maganin olsa wato gyambon ciki, idan mutum na son amfanuwa da kankana wajen maganin gyambon ciki wato olsa, sai ya rinka shanta kullum da safe kafin ya ci abinci.

  1. Yawan shan kankana na rage hadarin kamuwa da cutar ciwon zuciya.

Ga Amfanin ‘Ya’yan Kankana:

Mutane da dama basu san amfanin dake kunshe da ‘ya’yan kankana ba, kankana abin sha ne, magani ce, ‘Ya’yan da ke a cikinta ma maganine, akan Haka ne naga ya dace na gabatar da binciken masana Kan amfanin ‘Ya’yan Kankana ga lafiyar dan adam.

Duk lokacin da ka/kikasha kankana toh ka/ki daina yadda kwallan, maimakon haka sai ka/ki tarasu a waje daya ka/ki wanke ka/ki shanya a rana har su bushe, koh ka/ki siyo wadanda ake siyarwa a herbal medicine store. Zaka/ki dauki kwara 20 zuwa 30 sai ka/ki nike su, har sai sun koma gari (powder), sai ka/ki nemi ruwa misalin liter daya da rabi ka/ki zuba garin ka/ki tafasa sai ruwan ya tafasa, Shikenan hadin ya kammala.

Yanda Za’a Rinka Sha:

Zaka/ki sha sau 1 a kullum amma zaka/ki dakata a duk bayan kwana 3, Idan ka/kin sha na kwana 2 toh a ran na 3 ba zaka/ki sha ba, sai washe gari, a haka zaka/ki rinka yi har zuwa wani lokaci ya danganta da ciwon da ake son magancewa da kuma jimawar da matsalar koh ciwon da ke jikin mutum.

Kadan Daga Cikin Magungunan Yakeyi:

  • Samun zuciya mai koshin lafiya da rage yawan wasuwasi.
  • Yana maganin yawan zancen zuci.
  • Karawa garkuwar jiki karfi da kuzari.
  • Samun maniyyi mai rai da maganin karancin haihuwa ga namiji.
  • Yana gyaran ciki da hanji da wankin dattin ciki.
  • Yana haskaka fatar jiki tayi kyau da sheki
  • Yana taimakawa don saurin warkarda gyambo koh wani rauni a jiki.
  • Yana bada kariya daga barazanar kamuwa da ciwon suga, idan kana fuskantar wannan barazanar toh ka jarraba wannan maganin.
  • Yana rage nauyin jiki da kiba.
  • Sannan kuma maganine ga masu fama da anemia.
  • Yana lausasa bayan gari mai tauri koh karfi dake fita kamar na dabbobi.
  • Yana rage kumburin hanji, kumburin ciki, kumburin jiki dadai sauransu.
  • Sannan kuma ga samun karfi da kuzarin kasusuwan jiki.
  • Yana samarda jini ga jiki.
  • Yana wankin Koda da sauran datti.
  • Yana maganin ciwon jijiyoyinjin jiki.
  • Yana kare jiki daga barazanar yiwuwar kamuwa da ciwon daji.
  • Yana wargaza tsakuwar koda.

Wannan kadan ne daga cikin irin alfanun ‘ya’yan Kankana ga lafiyar jikin dan adam.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*