Hanyoyin Da Ake Sarrafa Kwai Kala Daban-daban Na Gargajiya Dana Zamani:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Ayau na kawo muku hanyoyin da zaku sarrafa kwai ne kala daban-daban nazamani dana Gargajiya wanda da yawa daga cikinmu bamusan wannan hanyoyin ba.

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Kwai
  • Nama
  • Curry
  • Maggi
  • Gishiri
  • Tumatir

Yanda Zaki Hada:

Zaki dafa kwanki, dai-dai yawan da kike so ki yanka shi kanana, ki yanka tumatir, attarugu da albasa akai ki yanka tafasasshen namanki kanana a kai, ki fasa kwan ki zuba akai, kisa maggi, curry, gishiri, ki kada ya kadu sosai, sannan ki dora mai a kan wuta ki soya kamar suyar wainar kwai, wannan kenan.

Yanda Zaki Soya Kwai Mai Nama Aciki:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • kwai
  • Nama
  • Maggi da gishiri
  • Curry
  • Albasa
  • Attarugu

Yanda Zaki Hada:

Zaki tafasa namanki da maggi, curry, thyme, albasa, ki daka shi ya daku sosai, saiki fasa kwai ki yanka albasa da attarugu, ki zuba dakakken nama, ki zuba maggi da gishiri dai-dai yanda kike so, ki kada sosai, ki soya kamar wainar kwai.

Yanda Zaki Hada Nama Cikin Kwai:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Kwai
  • Nama
  • Gishiri da Maggi
  • Albasa
  • Attarugu
  • Mai

Yanda Zaki Hada:

Zaki dafa kwai ki dai-dai yawan da kikeso, kowanne ki yanke kasansa wajen fadin kadan ki kwakule kwaiduwar a hankali ki cire ta, ki tafasa namanki da curry, thyme, maggi da gishiri, idan ya dafu saiki zuba attarugu kadan ki daka naman, sannan ki dinga debo dakakken naman kina turawa cikin kwai, idan ya cika sai ki debo kwaiduwar ki toshe bakin kwan da ita, haka zakiyi tayi har ki gama, sannan ki dinga tsoma kwan a cikin ruwan kwai kina soyawa, idan ya soyu sai ki kwashe, wannan naman cikin kwan shima yana da dadi sosai, ki gwada yinshi ‘yar uwa.

Yanda Zaki Wainar Kwai Da Alayyahu:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Kwai
  • Hanta
  • Alayyahu
  • Curry
  • Maggi da gishiri
  • Albasa da Attarugu
  • Manja ko Mai

Yanda Zaki Hada:

Zaki yanka alayyahunki ki yankata kanana-kanana, sai hantar ki daka ta, bayan kin dafe ki fasa kwai ki zuba hantar, ki zuba alayyahunki, curry, maggi, gishiri, da albasa, idan kina so, ki soyata kamar suyar wainar kwai.

Yanda Zaki Wainar Kwan Vegetables Da Koda:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Koda
  • Kwai
  • kabeji
  • Peas
  • Green peas
  • Carrot
  • Maggi da gishiri
  • Curry
  • Albasa da attarugu

Yanda Zaki Hada:

Zaki yanka vegetables dinki ki soya su sama-sama, ki fasa kwanki ki zuba maggi, curry, gishiri, ki tafasa kodarki ki yanka ta kanana-kanana, saiki zuba akan kwan, ki zuba vegetables ki soya.

Yanda Zaki Dafaffen Kwai Mai Dadi Kiyita Santi:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Kwai
  • Albasa da Attarugu
  • Curry
  • Maggi da gishiri

Yanda Zaki Hada:

Zaki fasa kwanki ta samansa amma fasawar yar karama zakiyi, ki zaggago kwan a kwano, saiki yanka attarugu da albasa ki zuba a kan kwan, ki zuba curry, gishiri da maggi dai-dai yanda dandanon zai yi miki, sannan ki zuba mai kadan ki kada kwan sosai, sannan ki duddura kwan a cikin kwaiduwarsu da kika juye, ki kawo solitef ki nannade kwan dashi sosai sai ki zuba ruwa a tukunya, ki jajjera kwan ki rufe ya dahu sannan saiki sauke, zaki bare kamar yadda ake bare dafaffen kwai, bayan kin warware solief din Shima yana dadi sosai.

Yanda Zaki Kosan Kwai:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Kwai
  • Busasshen burodi
  • Attarugu
  • Maggi da gishiri
  • Curry
  • Albasa
  • Mai

Yanda Zaki Hada:

Zaki daka busasshen burodi, ki fasa kwai, ki yanka albasa, attarugu, maggi, gishiri, curry, ki zuba busasshen burodi ki juya yayi kauri kamar kwabin kosai, ki dinga dibar kullin kina sawa a mai kina soyawa kamar kosai, idan yayi ja ki dinga kwashewa kina tsanewa da kwadanda.

Yanda Zakiyi Waran Kwai Da Alalen Kwai Mai Dadi:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Kwai
  • Kifin gwangwani
  • Albasa da attarugu
  • Maggi da gishiri
  • Man gyada ko butter

Yanda Zaki Hada:

Dafarko zaki bude Kifin gwangwaninki, ki dagargaza shi ya murmushe sosai, sannan ki fasa kwai dai-dai yanda kike son yawan alalan, ki yanka albasa, attarugu, carrot, ki hada da peas ki zuba akan kwan, kisa gishiri, maggi, curry, ki zuba kifin akan kwan, ki buga sosai, ki zuba mai kadan ki shafa butter koh mai a gwangwani ki zuzzuba, koh kuma ki kukkulla a leda, za ki iya ci haka idan ya dahu koh ki yayyanka kisa a ruwan kwai ki soya ya zama warar kwai.

Yanda Zaki Wainar Kwai Da Dankali:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Kwai
  • Dankali
  • Nama
  • Albasa
  • Curry
  • Maggi da gishiri
  • Mai

Yanda Zaki Hada:

Zaki dafa dankalinki ki marmasa, ki tafasa nama, curry, maggi da gishiri ki daka, ki tafasa kwai ki zuba dakakken naman da dankalin akan kwan ki yanka albasa, kisa gishiri, maggi da curry ki kada su hadu sosai ki soya kamar suyar kwai, koh kuma ki gasa a oven.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*