
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
A yau in shaa Allahu zanyi bayanine gameda yanda zaku Gujewa kurajen fuska gaba daya in shaa Allahu.
Ga Kadan Daga Cikin Abubuwan Da Suke Kawowa:
- Yawan wanke fuska:
dayawanmu muna da dabi’ar yawaita wanke fuskokinmu akai-akai, wasu sukan wanke fuskarsu a rana akalla sau shida koh fiye da hakan kuma da sabulu, toh wannan dabi’a tana kara janyo mana kuraje a fuskarmu saboda wa innan sinadaren da suke cikin sabulun suna wanke ainihin maikon da Allah ya sanya a fata, ta kasance ciki sannan sukan sa fata bushewa da kuma darewa, abinda ya kamata muyi shine indai zamusa sabulu a fuskarmu toh akalla mu wanke sau biyu kawai wato safe da yamma wannan shine. - Amfani Da Sabulu Mai Karfin Gaske: Dayawanmu mukan yi amfani da sabulu wanda yafi karfin fatarmu, misali medicated koh lightening soap, Wa innan sabulan suna dauke da sinadaran da suke kara sanya wa fuska ta samu matsalar fata musanmam ga wa inda dama can sunada pimples a fuskarsu, maimakon wayanan sabulai zaifi kyau mu samu sabulu wanda yake baida karfi sosai wato (beauty soap kamar irinsu joy, giv, dov, lux dadai sauransu) amma matukar zamu cigaba da amfani da sinadarai masu karfi akan fatarmu toh koh muna maganin kuraje, zasu rinka tafiyane suna kuma dawowa.
- Man Shafawa Mai Karfin Gaske: Suma man shafawa kamar sabulu, yana dakyau mu nemi wanda yayi dai-dai da yanayin fatarmu, misali in fatarmu mai saurin bushewa ce toh yana da kyau mu samu man shafawa mai dan maiko wanda zai rinka hana fatarmu saurin bushewa da tsagewa, haka in fatarmu mai maikoce, toh zaifi kyau muyi amfani da mai wanda baya daskarewa a jikin fuska saboda fatar ta samu damar shan iska yanda ya kamata.
- Kwakule Fuska Wato (kwantale kurajen): Wannan dabi’a ita tafi saurin janyo mana matsalar kuraje da kuma tabbai a fuskokinmu, dayawan masu fama da pimples basa rabo da wasa da hannunsu akan fuskokinsu, kodai suna shafa fuskar koh kuma suna fasa pimples din koh suna kwarzane kurajen, wannan yanasa kwayoyin cututtuka saurin shiga fata wanda yana daya daga cikin dalilan da suke kawo pimples, sannan yana sa kurajen suyi baki su bar mana alamar tabo wanda yakan dauki tsawon lokaci kafin ya bata.
- Rashin Wanke Hannu Akai-akai: Barin dauda ajikin hannu yana taimakawa matuka wajen kara jawo mana pimples a fuskokinmu, shi yasa yake da kyau mu rinka wanke hannayenmu kafin mu shafa mai koh wani maganin kurajen saboda da tafin hannunu muke yin kusan komai kama daga shara, ayyukan gida, taba wayoyinmu da dai sauransu, shiyasa in muna wanke hannu akai-akai sai mu guji karawa ciwo ciwo.
- Rashin Gyara Fuska Wato Dilka: Rashin gyaran fuska wanda zai taimaka wajen cire duk wani dauda da yake kan fatar mu na taimakawa wajen kara jawo mana kuraje, kamar yanda yawaita yin gyaran fuskarma zai iya kara mana pimples a fuskokinmu, dilka koh exfoliating hanyace da akebi wajen cire duk wani datti da mataccen fata wanda baida amfani akan fatarmu, ta yanda fatar tamu zata kasance da kyau, sheki, tsantsi da lafiya a koda yaushe, shiyasa yake da kyau mu rinka yawaita yin wannan akalla sau 1 a sati domin mu hana sababbin kuraje fitowa a fuskokinmu.
- Yanayin Abincin Da Mukeci: Abincin da muke ci yana daya daga cikin abinda yake kara jawo mana kuraje a fuskokinmu, kamar yanda mukasani yawaitar maiko a karkashin fata na daya daga cikin dalilan da suke kawo mana kuraje, shi yasa yana da kyau mu rinka ragewa koda bazamu iya daina cin nau oin abincin da suke dauke da maiko mai yawa wanda suke jawo mana pimples ba, misali abincin su hadar da kayan zaki irinsu cake, doughnuts, da dai sauransu, sai kuma masu maiko kamar irinsu gyada, magerine da dai sauransu.
- Yawan Shiga Rana: Yawaita shiga rana yana daya daga cikin dalilan dake sawa muyita maganin pimples amma yaki tafiya koda kuwa muna bin dokokin muna kiyaye cimarmu, shiyasa mafi akasarin masu fama da pimples yan matane wayanda suke yawaita fita makaranta, aiki da dai sauransu, yana da kyau in za’a fita cikin rana kar a shafa mai wanda yake da maiko sosai wato (oil) koh kuma ayi amfani da man kariya wato (sunscreen)
- Sai Kuma Yanayin Halitta: Bayan duk wa innan dalilai dana lissafa a sama akwai kuma wanda dama halittarsu ce kurajen fuska, wannan kuma yana faruwa ne saboda rashin daidaitar sinadaran halitta na jiki wato (homones) shiyasa wasu za kuga suna iyakar kokarinsu wajen kiyaye duk wayannan sharuddodin amma dukda haka pimples baya rabuwa da fuskokinsu, wa innan abinda ya kamata shine su samu likita dan ya sanar masu da kwayoyin da ya dace suyi amfani dashi wajen magance matsalar tasu.
- Lokaci: Pimples lokacine kamar yanda dayawan mutane suke fada, koda yake wasu harda rashin kiyayewa da bin sharrudan da na lissafa, amma mafi akasarin lokuta pimples yana zuwa ne dai-dai lokacin da matasa suke samun yanayin canji na girma a halittarsu wato puberty, sai dai wasu daga nan ne kuma in basa kiyaye sharuddan nan na sama sai su wuce dashi har girmansu.
- Bleaching: Bleaching koh shafe-shafe na daya daga cikin manya-manyan dalilan da suke kawo kurajen jikin fuska, kuma wannan shi yafi koh wanne muni domin shi zai fito manya-manya sannan yasa fuskar tai jirwaye ta kuma yi tabbai koh ina, shi yasa yana da kyau mu guji yin amfani da duk wani mai ko sabulun da zai sanyamu haske domin suna kona mana fatane kawai su kuma baiwa cututtuka damar shigar mana fata.
Wa innan sune kadan amma kuma manya-manyan dalilan da suke jawomana kuraje a fuska ya zamana munata magani amma bama samun canji, da fatan zamu kiyayesu.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply