Kadan Daga Cikin Amfanin Turaren Miski A Farjin Mace Da Jikinta Da Kuma Yanda Zatayi Amfani Dashi:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Shi turaren almiski turare ne mai dimbin tarihi da asali, ya kasance turare mafi shahara da yayiwa dukkanin sauran turaruka fintin kau kama daga fannin kamshi, yin suna sannan kuma da amfani.

Sai dai kuma akwai karancin ilmin sanin amfanin almiski wanda zaka tarar mutane kalilan ne suke da masaniya a kan amfaninsa wannan ne yasa bakowa ke amfani dashi ba saboda basusan ya zasuyi amfani dashi ba.

Sannan kuma yana da matukar amfani musamman ga mata domin yana sanya nishadi da annashuwa, haka kuma yana janyo hankalin miji zuwaga matarsa wannan shine.

Kuma a kasashen larabawa amfani da almiski ya zamo musu al’ada a garesu domin duk wata matar da zata yi aure koh wacce tayi aure zaka tarar tana mai amfani da almiski wato (Musk tahara) wannan bai rasa nasaba da sanin muhimmancinsa da sukayi ba.

Yana da kyau sosai a tarar da mace tana amfani dashi maimakon amfani da turarurrukan nan da basa da wata fa’ida face kyalkyali da tsada a kawai kuma ba wani amfanin da zaiyi musu koh da ma kuwa zaiyi musu toh badai kalar na Miski ba.

Shi turaren almiski launinsa ya kasu kashi 3 ne, akwai fari mai kamar madara mai kauri (white musk) shi wannan baya saurin narkewa kuma kuskure ne mace ta sanya shi a farjinta, Idan koh aka saka shi toh bazai narke ba kuma wasu illolin zasu iya faruwa da mace, sai dai a shafa shi.

Akwai fari kal mai kamar ruwa kamshinsa daya ne da mai kaurin amma shima kada mace ta sanya shi a gabanta dan da sinadaran dake da illa musamman a wajen da aka saka shi, toh a maimakon haka sai a tarfa shi ga cotton a shafa a kan pant wannan zai baki wani siiri na musamman domin a duk inda mijinki yake da zaran yaji kamshin wannan turaren koda a kasuwane koh kuna a cikin jama’a ne toh zai tuna dake kuma zai ji shawarki, kinga kenan zaiyi zumudin ya dawo dan saduwa dake, Kinga kuwa kenan anan turaren miski yayi amfani.

Sannan akwai jan almiski shi wannan masu fama da aljanu suke amfani da shi, yana fatattakar aljanu da yardar ubangiji, amma a kanyi rukiyya wa mai iskan sai ayi amfani da turaren, idan ba ayi rukiyyar ba toh mai iskan zai kyamaci turaren ta yanda koh ganin almiskin baya son yayi.

Anan idan za’ayi amfani da Almiski sai ayi amfani da (Musk tahara) a nemi wanda aka yoshi daga Makkah koh Pokistan koh kuma India.

Akwai sunaye daban-daban da ake yiwa musk tahara kamar su musk Aljism, haka kuma akwai musk Aishat wanda aka ruwaito Aishat (r.a) tayi amfani dashi kuma ta kwadaitar da amfani da shi din.

Musk tahara koh musk Aishat Shi yafi dacewa mata su rinka yin amfani dashi dan karin tagomashin zamantakewa da kuma tsabtace jiki, idan aka tafasa lalli aka tarfa miski sai ayi sith bath da shi yin hakan zai magance wa mace Warin gaba.

Sai kuma kaikayin gaban mace, yana kashe kwayoyin cuta a gaban mace, Kuma yana rage yawan majinar gaba a sanadin wata cuta, yana tsabtace mahaifa musamman idan aka dage da amfani dashi, idan kuma mace ta haihu toh zata iya neman ganyen magarya sai ta tafasa ta tarfa miski ta rinka amfani dashi a hakika wannan nada faida sosai, turaren almiski ana maganin farfadiya dashi, sannan kuma yana maganin cutukkan kwakwalwa wato (brain disoders)
yana maganin bibiyar aljannu, Kuma yana sanya mai gida ya rinka sha’awar matarsa, yana maganin warin kashi ga maza da mata suma, kuma yana hanawa aljanu bibiyar mace musamman wadanda ke saurin shiga a gaban mace a wani ilmin kuma akan tarfa madaran tinfafiya a gauraya da farin almiski a shafawa jiki koh ga6ar da take ciwo a sanadin iska koh aljanu masu shanye sashin jiki.

Saboda haka mata sai a kula bafa dagwala yatsa za ayi a cusa turaren a cikin gaba ba, a’a zaki nemi cotton ki dan tarfa turaren sai ki shafa akan pant dinki, cusa turare a gaba yana da illa sosai, don haka sai a kula adaina jin kunyar neman ilmi ba kunya wacce ta wuce maigidanki ya kusance ki amma yaji kina wari haba! Wannan faduwar girmane gaskiya.

Abinda yafi dacewa ace mace tana da hulba, lalli, kwalli, turare, sabulun magarya da zuma a cikin kayan da take amfani dasu a gidanta gaskiya.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*