Muhimman Abubuwa Guda Bakwai (7) Da Suke Iya Lalata Gaban Mace:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

A yau in shaa Allahu zan kawo muku yanda zaku kiyaye wadannan abubuwan Da suke lalata farjin mace wanda yakamata kusansu sannan kuma ku kiyayesu.

Da akwai wasu halaye da dabi’u da mata da dama suke aikatawa wa’inda suke iya cutarda gabansu sannu a hankali ba tare dasu sun san wadannan abubuwan ba.

Mafi akasarin mata da suke aikata wadannan dabi’un koh dai suna sane suke aikatasu koh kuma akwai jahiltar illar abinda suke yi.

Ga wasu dab’iun guda bakwai da suke iya lalata gaban mace saboda a kula da kuma gujewa aikatasu.

  1. Yawan wanke farji wato gaba da kowanne irin sabulu, akwai mata da dama da suke amfani da duk wani sabulun wankan da suka samu domin tsaftace farjinsu toh a maimakon haka suke illata kansu saboda rashin sanin irin sinadarin dake kunshe cikin wadannan sabulan da mata ke wanke gabansu dasu saboda akwai chemical din da Ake hada sabulun dasu wanda sune suke illata wa mata farjinsu a sannu a hankali, mafi akasarin sabulan dake canza launin fata toh suna dauke da sanadaran da suke yiwa gaban mace illa, saboda haka sai mata ku kiyaye.
  2. Sannan zama da jikankken kaya musamman matan da suke shiga rafi wanka koh tafkin wanka na zamani wato (Swee min fool) koh kuma ruwan sama ya daki mace har tayi irn tsamo-tsamo dinnan a jike toh a irin wannan yanayin muddin mace na zama na tsawon wani lokaci da jikakken kayan a jikinta toh kuwa lallai wannan yana haifarda warin gaba kuma yana iya sawa mace illa idan bata kula, saboda cututtuka na bacteria da zai iya shiganta.
  3. Sai kwanciyar bacci da matsattsun wanduna, wasu matan suna kwanciya ne da kayan dake matsattsu sosai, wanda yakan hana iska ratsa farjinsu, wanda yin hakan ba dai-dai bane, rashin samun giftawar iska a farjin mace na iya baiwa kananun cututtuka daman shiganta, shi yasa likitoci da dama suke bada shawaran mata su daina kwanciya da kaya a jikinsu koh kuma su rika saka wandunan da zasu sha iska dasu.
  4. Sai kuma yawan shan madaran yogurt ga mata babban illah ne amma mata da dama sun daukeshi abun shansu, a cikin sinadaren da ake hada madarar da ita an gano wasu masu dauke da sinadaran dake ciki da kai tsaye suke yiwa farjin mace illah, idan mace tana yawan sha toh yana iya sa gabanta ya rinka yin wari, madara da cin kayan itatuwa sunfi amfani a jikin mace sosai a maimakon yogurt.
  5. Sai shan taba, wiwi koh kuma shisha, suma wadannan nan shaye-shayen kai tsaye suke lalata gaban mace saboda hayakin dake shiganta, shi hayaki kai tsaye yake shiga jikin mutum kuma ya zauna a ciki, shi yasa duk mai shaye-shaye irin na hayaki kana ganinsa zaka ganeshi, musamman taban sigari yana dauke ne da abunda yake jawo warin gaban mata.
  6. Sai rashin canza audugar al’ada wato ( parts ) koh tsumma akan lokaci, toh shima yana da kyau mace ta rinka canza kunzugun al’adanta daga lokaci zuwa lokaci domin gudun kamuwa da cututtuka, a kalla duk bayan awanni 3 zuwa 4 mace ta canza kunzugunta.
  7. Sannan yawan kula yayin wanke farji, da yawa daga cikin wasu matan idan sun tashi tsaftace gabansu suna cusa sabulu har can ciki wanda yin hakan yana yiwa gaban mace illah sosai, waje wajen gabanki, wajen lungunan dake saman farjinki duk sune abinda zaki kula dasu wajen tsaftacewa da sabulu wannan shine.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*