Sabon Hadin Da Yake Maganin Ciwon Sanyi Kowacce Iri Ce:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

‘yan uwa inason ku daure kuyi wannan hadin yana magance Cutar sanyi sosai da ikon Allah.

Shekaru da dama ana amfani da tazargade wajen magance manyan cututtukan da suke damun al’umma domin tana da sindarai wadan da suke kashe cututtuka da dama a jikin dan Adam kuma a cikin kankanin lokaci.

Ku biyoni kuji kadan daga cikin amfanin shayin tazargade da kaninfari.

  1. Yana magance ciwon kai mai tsananin gaske
  2. Yana magance zazzabin maleria mai zafi.
  3. Sannan har illa yau yana magance bacin ciki.
  4. Yana magance zafin zuciya kaji zuciyarka na Yi maka zafi toh duk yana maganceshi.
  5. Yana maganin infection.
  6. Yana magance raunin mazakuta ga maza.
  7. Sannan yana karfafa garkuwar jiki.

Da dai sauran cututtukan da ban ambacesu ba.

Yanda Za’a Hada Shayin Kuwa Shine:

Za’a samu garin tazargade teaspoon daya kaninfari rabin teaspoon a hada da ruwa kofi biyu a dafa, kuma za’a iya saka suga kadan koh kuma zuma a ciki.

A kowacce Rana kofi biyu a sha kofi daya safe kofi daya da yamma ayi kamar kwana 7 anayi in shaa Allahu za’a samu waraka.

Sannan kuma ana iya jikawa shima yanayi kamar kwana 2 musamman masu infection, amma ba’a son a cika shan shi saboda yanada daci kuma koda batason daci.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*