Sabon Hadin Maganin Matsi Na Musamman Domin Uwargida Mai Saukin Gaske

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Akwai mata da yawa da suke fama da wannan matsalar ta budewar gaba, wasu In sun haihu wasu kuma in suna hawa keke mai taya 2, yayinda wasu kuma In suna tsalle-tsalle, wasu kuma in anyi musu fyade da dai sauransu.

Toh idan kina Buƙatar gabanki ya tsuke yadawo tamkar na yarinyar wacce batasan namiji ba a rayuwarta toh ga matakan da zaki bi nan

Na Farko:

  • Bagaruwa ta hausa.
  • Ganyen magarya.

Idan kika samu wadannan abubuwan saiki dafasu, koh kuma ki dafa ita bagaruwar ita kadai, sai ki rinka wanke gabanki da ruwan, koh ki zuba a baho ki rinka zama a ciki da dumin duminshi kaman minti talatin, kiyi haka a kalla kamar sau 2 a sati.

Sai Na Biyu:

  • Kaninfari.
  • Zuma amma.

Idan kika same su saiki dafa da zuma, ki rinka shanshi da zafi-zafinshi, koh ki jika shi ya kwana da safe ki tace kisha da madara da zuma.

Na Uku:

  • Kaninfari.

Zaki kuma dafa shi kaninfari ki rinka zauna a ciki da dumi-duminsa koh a rinka tsarki da ruwan koh kuma ki zuba kaninfari a garwashi wato rushi ki rinka tsugunnawa, kiyi turare, shima sau biyu a sati zaki rinka yi.

Ga Na Hudu Kuma:

  • Kwallon mangwaro.
  • Zuma mai kyau

Idan kika samu kwallon mangwaro saiki fasa shi, zaki ga dan cikin fari, sai ki shanya shi ya bushe, idan ya bushe sai ki daka shi, ki kwaba da zuma ki rinka sashi a gabanki da daddare bayan isha’I, amma idan zaki kwanta bacci saiki wanke gaban naki sosai.

Na biyar:

  • Koh kuma ki dafa dan cikin da bagaruwa, ki wuni kina tsarki dashi, koh ki zuba ruwan a baho saiki rinka zaunawa a ciki shima a kalla sau 3 a sati.

Sai Na Shida:

  • Bagaruwa
  • Chukwui

Idan kika samu bagarauwa saiki shanya shi ya bushe, bayan ya bushe saiki daka ki tanka de kayarki, ki samu Chukwui, kina Dandala da shi kina ci, in shaa Allahu zakisha mamaki kikayi daya daga cikin wannan hadin.

Abinda Ake Nufi Da Chukwui:

Shi chukwui wani nau ine na dabino wanda ba’a fiye nomashi akasar hausa ba, amma bayida wahala akasuwa, shi din zaki ganshi yanuna sosai kamar anzuba miahi zuma saboda tsabar taushinsa da zakinsa, kuma manya-manya ne shi.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*