
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wa sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com
Ayau in shaa Allahu zan kawo muku yanda zakuyi hadin Sabaya ne domin ciko da Nono tsayarwa Gyaran nono gaba daya dai nake nufi.
Dole ne duk inda mace take tohta matso kusa ta jarraba wannan hadin domin In shaa Allahu za tayi mamakin yanda jikinta zai gyaru musamman ma nonon da aka shayar da yaro dashi.
Wannan hadin da zan bada yana da matukar amfani ga jikin mace, amma Kuma sai masu hakuri da bin ka’idar sha ne kadai za su rabauta da wannan hadin gaskiya.
Abubuwan Da Ake Buƙata:
- Waken suya gwangwani 4.
- Alkama gwangwani 4.
- Dawa gwangwani 4.
- Shinkafar tuwo (farar shinkafa) gwangwani 4.
- Ridi gwangwani 4.
- Agushi gwangwani 4.
- Aya gwangwani 4.
- Gero gwangwani 4.
- Gyada me bargo gwangwani 4.
- Hulba gwangwani 2
Duk abubuwan nan dana lissafo kar a tambaye ni a soya dan ban ambaci soyawa a ciki ba.
Dafarko zaki hade kayan dake sama gaba daya, bayan kin tabbatar da tsaftacewarshi sai ki Kai a nika Miki su suyi laushi sosai
Sai ki samu ruwa 75cl ki daura a wuta sannan ki debi garin da aka nika ki dama da ruwa 25cl ki zuba a kan ruwan dake wuta bayan ya tafasa, sai ki rufe ki bashi a kalla yakai minti 10 zuwa 15 sannan ki tabbatar da ya dahu ki sauke ki saka madara kisha da safe kan kici komai da rana kan kici komai da dare in zaki kwanta ma haka.
Sannan kima ba a dafawa da yawa ace za’a ajiye saboda zai tsinkene, idan miji na fama da rama koh rashin ruwan maniyyi yana sha sau daya kullum idan yaro na rama koh za’ayi mashi yaye shi a bashi sau 3 kullum idan be karbe shi ba yana saka shi kashi a cire hulba da madara In shaa Allahu zai daina.
Sai kuma mata masu son suyi kiba suma su sha matan da iya nono suke so ya gyaru su cire number 1 to 5 suyi ragowar sauran.
Ga Wani Sabon Hadin Sabaya Shima
Abubuwan Da Zaki Buƙata:
- Alkama
- Waken Soya
- Danyar Shinkafa wato (farar shinkafa)
- Gyada (kamfala)
- Ridi
- Hulba
- Madara
- Zuma/Sugar
Alkama, farar shinkafa da waken suya dukansu kwano dai-dai, sai kuma ridi, gyada da hulba rabin kwanon kowannensu.
Yanda Zaki Hada:
Zaki jika alkama da farar shinkafa waje daya har na tsawon awa biyar shi kuma gyada da ridin zaki hadesu waje daya ki soyasu, sama-sama ki bushar da bawon gyadar, sannan sai ki tsame shinkafa da alkaman nan idan sun tsane sai ki hadesu da wannan soyayyen ridi da gyadan da waken suya da hulba kikai inji a niko miki.
Toh idan an kawo garin sai ki rinka dama cokali 3 kullum safe da yamma kina sha, Amma wajen damawar zaki dama ne kamar zakiyi talge, idan kin sauke sai kisa madara da zuma koh sugar ki ringa sha.
Ga Kunun Sabaya:
Abubuwan Da Zaki Buƙata:
- Farar shinkafa (shinkafar tuwo) gwangwani 1
- Alkama gwangwani
- Waken suya rabin gwangwani
- Riɗi gwangwani 1
- Gyaɗa mai bargo gwangwani 1
- Gero gwangwani 1
- Garin Hulba rabin gwangwani
- Garin dabino gwangwani 1
- Garin aya gwangwani 1
Yanda Zaki Hadasu:
Zaki jiƙa gero da daddare se dasafe ki shanya, sannan ki jika shinkafa da alkama na tsawon awa 5 sai ki tsame ki shanyasu, kibarsu susha iska, saiki soya gyada sama sama
ki soya riɗi kamar zakiyi kantun gana, sai ki tsince waken suya ki gyara kisoyashi sama-sama, saiki hada su duka guri daya ki kai a nika miki sannan ki haɗa garin aya da dabino aciki, sai ki dinga dama cokali 3 da ruwan zafi kamar kunu kina sha da madara, kullum Zaki rinka sha amma safe da yamma.
Wannan hadin yana hana rama sosai, Kumw kowa yana iya sha
Kamar masu ulsa da maza da mata da yara da tsofaffi har da mara lafiya da kuma masu ciki, sannan kuma yana gyara jiki ta ciki data waje.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply