
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
Wato lalli na daya daga cikin kayan abubuwan da ake amfani dasu wajen yin ado da zayyana a jikin dan Adam, baya ga kwalliya da ake yi da shi.
Baya ga kwalliya da ake yi da shi, Kuma lalli na dauke da sinadarai masu amfani da tarin yawa.
Ga kadan daga cikin amfanin lalli da muka dan zakulo muku:
- Ciwon kafa: Yin lalli na rage ciwon kafa sosai za’a kwaba lalli da ruwa yayi kauri, a shafa wa kafar na tsayon lokacin da ake bukata sannan a wanke. Yin haka nasa kafa yayi sauki, sannan yana rage radadi da zugin dake damun mutum a kafarsa.
- Dattin ciki: Shan ruwan lalli na wanke dattin dake cikin ciki, Idan aka jika lalli da ruwa aka tace, sai a sha ruwan dai-dai gwargwado, Shima yin hakan yana wanko dattin ciki.
- Sai kuma gyaran fata: Ana amfani da lalli wajen gyaran fatar jiki da kawar da datti da kuma sanya fata haske mai kyau, a saboda haka, sai a zuba lalle da ruwa a rinka wanka da ruwan lallin akalla sau daya a rana.
- Sai fatar fuska: Lalli na sa fuska ta yi laushi da haske. Bayan an kwaba lallin da kauri sai a rinka goga fuskar da ita, sai yayi kamar bayan minti 20 zuwa 30 sai a wanke fuskar da ruwa, za’a iya yi sau 1 zuwa 3 a rana.
- Masu fama da kurajen fuska: Ga masu fama da kurajen ‘pimples’ sai su kwaba lalli da ruwan lemun tsami yayi kauri saisu rinka shafa kwabin a fuskar. Zuwa dan wani lokaci pimples din zasu bace gaba daya.
- Amosanin kai: Ana wanke gashin kai da ruwan lalli domin maganin amosarin gashi, sannan kuma ana yin hakan ne ta hanyar kwaba lalli a ruwa yayi dan ruwa-ruwa sannan a jika gashin a cikin ruwan. Bayan kamar minti ashirin sai a wanke kan, yawan yin hakan yana kashe amosanin kai gaba daya.
- Gyambon yatsa: Masu gyambon yatsa wato (dankankare) na amfani da lalli wajen neman sauki, shima akan kwaba shi a sanya a wurin da ke da gyambon a yatsar domin neman waraka koh busar dashi.
- Kwalliyar gashi: Maza da mata na amfanin dashi wajen kwaliya a gashin kansu da kuma gemu, sai a kwaba lalli da ruwa a shafa a waurin da ake bukata na ‘yan mintoci sannan a wanke shi.
- Zayyana fata: Ana kuma amfani da lalli wajen yin ado ta hanyar zayyana a fatar ji, ana kwaba lalli yayi kauri, sannan a lika leda mai dauke da nau’in zayyanar da za a yi a fatar, sannan a shafa lallen a sama. Daga nan sai a bar shi yayi awanni kafin a wanke. Ana kuma iya yin zayyarar kai tsaye da kwababben lallin ba tare da sanya ledar ado ba.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply