Wasu Daga Cikin Abubuwan Da Suke Mace Daukar Ciki:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Juna biyu wato Daukar ciki abu ne wanda ma’aurata suke nema da zaran an daura aurensu.

Sau tari a wani lokaci ana samun matsalar rashin samun juna biyu kuma wannan yana kawo matsaloli da tashin hankali tsakanin da yawan ma’aurata.

Rashin samun ciki na iya kasancewa daga bangaren mata koh kuma namiji, ina nufin ba duk rashin samun juna biyu ke zama laifin mace kadai ba wani zubin laifin mijin ne.

Ayau zanyi bayani ne gameda abubuwan da suke iya hana mace daukar ciki da suka shafi mace kadai, zan kawo na mazan suma in shaa Allahu.

  1. Matsalolin al’ada wato period, idan mace ta kasance al’adar ta baya zuwa a lokacin da yakamata koh kuma ta kanyi kamar wata 3 koh 4 bata ga al’adarta ba toh lallai tana iya samun rashin daukar ciki da wuri, wannan matsala na bukatar a tafi asibiti domin ayi mata gwaje-gwajen jini domin duba yawan sinadaran hormones dake acikin cikin ta, saboda ita wannan matsalar ana iya shawo kanta da ikon Allah.
  2. Tsufa koh kuma yawan shekaru ga mace, daukar cikin farko bayan mace ta haura shekaru talatin na iya zuwa da wasu matsaloli kamar zuban ciki da haihuwar yaro mai wata nakasa, wato a lokacin da mace ta keda shekara Goma sha bakwai koh abin da yayi sama amma bai kai talatin ba toh tafi samun ciki mai lafiya, domin tana da cikakkar lafiyar samun ciki cikin sauki.
  3. Endometriosis Wani nau’in rashin lafiya ne wanda kan iya sa wani bangaren mahaifa yai kauri da karfi ta yanda zai hana kwan namiji da kwan mace su hadu, kuma hakan kan iya hana mace daukar ciki, Amma ana iya gano wannan matsalar kuma a magance ta a asibiti da yardar Allah.
  4. Kiba mai yawa koh kuma rama mai yawan gaske ga mace, idan mace ta na da kiba sosai koh kuma mace tana da rama sosai ta na iya daukar tsawon lokaci kafin ta dauki ciki, da akwai gwaje-gwajen da za’a yiwa mace a asibiti kuma aba da shawarwari koh kuma magani a asibiti.
  5. Rashin ni’ima koh ruwan bakin mahaifa, shima idan bakin mahaifar mace ya kasance busasshe yana iya hana kwan da namiji samun sukunin shiga mahaifa bayan saduwa, wannan yana iya hana mace daukar ciki shima.
  6. Infection wanda ba ayi maganin shi ba, da akwai mata da dama masu infection amma basa shan magani akan ka’ida, toh a irin wannan halin infection din na iya mamaye mahaifa koh kuma ya mamaye maran mace kuma ya hana ta daukar ciki
  7. Matsalolin halittar mahaifa koh toshewan mahaifa idan mace ta na da fibroid, wannan a asibiti za’a tabbatar da shi kuma a bada magani koh kuma ayi wa mace theatre.
  8. Yin allurar ‘planning’ koh kuma shan maganin gargajiya na hana haihuwa ba tare da qa’ida ba, yana iya janyo haihuwar ta tsaya gaba daya.
  9. Ciwon sanyi wato ‘Infection’, shima idan yayi muni ya kan iya hana mace daukar ciki koh cikin ya dinga zuwa da matsaloli da dama.
  10. Matsalar Aljanin dare wato Jinnul Ashiq koh kuma ayiwa mace asirin hana haihuwa, wanda za mu kawo bayani akansa in shaa Allah.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*