
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com
A wani bincike da aka gudanar sannan kuma aka wallafa a mujallar “International Journal of impotence research, a shekara ta 2007”, yayi nuni da cewa matan da suke yawaita cin kayan marmari da kayan lambu musamman ganyayyaki sunfi takwarorinsu da ba sa yawaita cin dangogin wadannan abincin ingantacciyar lafiya, karfin sha’awa da kuma ni’imar gamsar da mai-gida.
Kankana: Ita kankana tana daya daga cikin dangin abinci mai karawa mata ni’ima da sha’awa, ba komai yasa ta wannan aikin ba kuwa face wani sanadari dake taimakawa wajen tausasa hanyoyin jini, hakan kuma sai ya bayu wajen gudanuwar jinin zuwa ga sassan jiki harma da al’aurar mace, hakanan kankanar ta ke kara ni’ima ga mata, a saboda hakane a yayinda abu biyun nan suka hadu, tohfa uwar gida ba sai an fada ba, don ana son kisha kankana mintuna 30 kafin kukaiga yin jima’i, kuma idan kina son samun cikakken aikinta saiki cinye harda wannan farar tsokar bayan kin shanye gurin zakin ke nan, abin da yasa nace haka kuwa shine, masana sun tabbatar da cewa, shi wannan sinadarin yafi yawa a cikin farar tsokar, koma bayan wannan jan wato me zakin.
Dabino: Shima dabino yana da matukar amfani ga rayuwar ma’aurata, amfaninsa kuwa bai tsaya ga iya mace ba, harma dashi namijin, saboda binciken da masana suka gudanar akan dabino ya bayyana cewa yana kunshe da sanadarai da yake kara yawan maniyyi da kuma ingancin sa, ba karin sha’awa ba kadai, ana iya amfani da dabino don gusar da matsalar raunin mazakuta na maza, sannan sun kara da cewa yana da wasu sinadarai dake karawa namiji kuzari ita kuma mace ya kara mata girman nonnta, da suke bayyana yanda za’a fi cin gajiyar aikinsa, sun ce a jika kamar guda bakwai koh kuma guda takwas a ruwa a barsu harna tsawon awa uku sannan aci, ina fatan zaku jure yin hakan.
Zuma: Tun a shekaru da yawa da suka wuce mutane ke amfani da zuma don inganta rayuwar aurensu, hakazalika a wannan zamani da muke ciki ana iya amfani da zuma don samun wannan fa’ida, saboda ita zuma tana da wani sanadari da ake kiran sa da (boron) wanda ke sarrafa wasu sanadaran halitta a jikin mace da ake kiran sa (estrogen) dashi kuma ya ke saurin motsa sha’awrta, wadannan su ne Kadan daga cikin nau’ikan abinci da muka zakulo muku don inganta rayuwar aure tsakanin ma’aurata.
Kuma a kullum ina jan hankalinku cewa, ba dole ne a hada dukkanin wadannan dangin abinci ba, a’a za’a zabi wanda aka ga za’a iya ne kuma yafi saukin samuwa ga mutum, Allah yasa mu dace, aamin yaa hayyu yaa qayyum.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply