
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
Akwai wasu ganye guda hudu da suke da matukar muhimmanci a jikin ‘ya mace wanda ba Kowacce macece ta sansu ba, toh yau in shaa Allahu zan kawo muku su domin wa inda basusansu ba su sani yanzu kuma suyi amfani dasu.
- Akwai Magarya: ganye na farko a ƙasar hausa wanda bai kamata mace tayi wasa dashi ba shine ganyen magarya, ana masa laƙabi da antioxidants wanda idan ana maganar tsaftar gaban mace wato farjin mace a sauƙaƙe toh babu wani ganye sama dashi, ki zuba ganyen kaɗai a ruwa ki dafashi sannan kiyi sit bath wato ki zauna a cikin ruwan harna tsawon mintuna goma sha biyar, wannan zakiyi shine bayan kinyi al’ada don gudun kamuwa da duk wata cuta sannan zai taimaka miki ki dawo da martabar kanki in shaa Allah.
- Zogala bazai taba yiwuwa ace ka samu mace wanda batasan ganyen zogala ba, saidai yanda ya kamata mace tayi amfani dashi ya amfaneta shine matsalar don Bata saniba, domin sarrafa ganyen zogala ƙaramin kuskure zai iya ɓatawa mutum ciki wato (gudawa) don haka idan kinaso kici moriyar ganyensa kawai ki busar dashi a inuwa sai kiyi garinsa kinasha a nono koh madara , zai ƙara miki ni’ima sannan ya ƙara miki lafiya koda kuwa kinada juna biyu wato Kinada ciki musamman wanda ya haura wata biyar (5)
- Gwaiba: A kyauta zaki iya samun ganyenta saboda ba wahala take dashiba, amma idan so kike ki kare kanki daga daukan ciwon sanyi tohki rinka tafasa ganyen kina zama aciki kamar yanda zakiyi da ganyen magarya, domin ganyen gwaiba asalin riga kafi ne babba wanda yana daga cikin ganyen Anticancer wanda shansa yake hana kamuwa da ciwon daji.
- Kuka: Ba iya kaɗa miya ake da kuka ba, manyan sirrikan dake jikin bishiyar kuka wajen mata da maza yakai a rubuta littafi guda akan kuka, amma idan mace na bukatar hanyar samun ni’ima a sauƙaƙe da ganyen kuka musamman wanda ya bushe a inuwa toh ta zuba garin a ruwan zafi sannan ta zuba madara ta gari koda sau ɗayane tasha a rana ya wadatar idan kika gwada yinshi zakisha mamaki kuma zaki godemin.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply