Yanda Ake Amfani Da Kuka Wajen Kara Karfin Mazakuta Ga Maza Da Kuma Karin Ni’ima Ga Mata:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Magungunan Da Kuka Yakeyi Sune:

  • Kuka tana maganin zazzabin maleriya sosai.
  • Sannan kuma kuka tana maganin tarin fuka wato (TB).
  • Kuka tana kara inganta garkuwar jiki.
  • Kuma kuka tana kara jini a jikin mutum.
  • Kuka tana maganin gudawa wato zawo
  • Kuka tana maganin ciwon hakori.
  • Kuka tana maganin ulsa wato gyambon ciki.
  • Kuka tana rage kiba.

Baya ga wadannan magungunan Da kuka takeyi, malama maijidda tace idan ana shan kuka ba zai sa mutum ya samu kumburin ciki ba, saboda rashin narkewar abinci sakamakon sinadarin fibre dake cikinta, haka kuma ga wadanda suke son rage tumbi suna iya shan ganyen kuka domin tana narkar da kitse sosan gaske.

Masaniyar tace kuka tana maganin ciwon ulsa, “ga mai fama da ciwon ulsa zai kada ganyen kuka a ruwa yasha, cikin lokaci kankani zai samu saukiin ulsa” da izinin Allah.

Kuka Tana kara Ni’ima ga mata da kuma Karfin mazakuta ga maza, masana sunce, saboda tasirin kuka wajen inganta ruwan jikin mutum, tana kuma tasiri wajen kara ni’ima ga mata.

Yanda ya kamata mata suyi amfani da kuka, za’a samu sassaken kuka a wanke sosai sai dinga sha kofi 1 da safe kofi 1 da yamma, sannan kuma kuka tana kara wa maza karfin jiki da mazakuta, haka kuma mazan da ke son jikinsu ya bude toh kuka tana taimakawa saboda sinadaran da suke a cikinta.

Yanda yakamata ayi amfani da kukan, ana busar da ganyen kuka a nika a tankade a yi miya domin cin tuwon dawa koh masara koh shinkafa koh tuwon alkama, kamar yanda nayi bayani tun a farko cewa kuka tana da matsayi musamman a abincin hausawa.

Hausawa suna yin miya da ganyen kuka, ana busar da ganyen kuka a nika sannan a tankade a yi miya domin cin tuwon dawa koh masara koh shinkafa koh kuma tuwon alkama, haka kuma Hausawa sukan yi amfani da kuka wajen yin danwake, amma masana sunce danyen kuka ya fi amfani fiye da busashen garin kukan da ake yin miya dashi.

Yanda ake busar da kuka yana kashe wasu sinadaran dake kunshe a cikinta, saboda rana da aka shanya kukar tana kone sinadarai da dama, saboda haka danyen ganyen kuka yafi amfani fiye da busashen garin kukan karin lafiya da sinadarai a cikin miya, sannan ba’a son idan za’a yi miyan kuka a bari ta sha wuta sosai domin yawan dafuwan yana rage yawan sinadaran da suke cikin kuka.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*