Yanda Ake Gyaran Jiki Da Gishiri Fatarki Tayi Kyau Musamman A Lokacin Sanyi:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com

Yin amfani da gishiri wato (salt) wata hanya ce ta gyaran jiki, sannan kuma a lokaci guda yana kawar da gajiya da kuma bada kuzari, saboda tarihi ya nuna cewa tun shekara ta 3150 kafin zuwan Annabi Isa alaihissalam al’ummar dake kasar masar suke amfani da ruwan teku mai dauke da gishiri wajen inganta lafiyar jikinsu, a shekara ta 400 kafin zuwan Annabi Isa alaihissalam kuma mutanen kasar Girka suka fara amfani da gishiri wajen gyaran jiki, al’amarin ya rinka tafiya da zamani wanda har zuwa yau ake kara fito da sababbin hanyoyin amfani da gishiri wajen gyaran jikinmu.

Toh a wannan makon na taho muku da matakan da zakubi wajen amfani da gishiri don gyaran jikinku.

Sannan akwai bukatar ki samu gishirin da ake kira (sea salt) koh kuma (rock salt) wannan gishiri yana kunshe da sinadarin ‘sodium’ da kuma ‘chloride’, sannan ki nemi gishirin da ake kira (Epsom salt) wannan gishirin yana kunshe da sinadarin ‘magnesium’ da kuma ‘sulfate’, haka kuma zaki nemi gishirin da ake kira da (dead sea salt) wannan gishiri yana kunshe da sinadarin ‘magnesium’ da ‘sodium’ da ‘calcium’ da ‘potassium’ da ‘chloride’ da kuma ‘bromide’, sannan ki nemi bakar soda, mai kunshe da sinadarin ‘bicarbonate’, sai kuma man ‘essential oil’, amma sau da dama mutane suna amfani da sinadarin Borad a matsayin kayan hadi lokacin da suke hada sinadaran da zasu sanya a ruwan gishiri don gyaran jiki, toh gaskiya amfani da sinadarin Borad yana haifar da matsala a jiki yakamata a kiyaye.

Abubuwan Da Zaki Buƙata:

Zaki samu cikin kofin shan ruwa na gishirin (rock salt) cikin kofin sha ruwa 1 na gishirin (epsom salt) sai kuma cokali 2 na bakar soda.

digo 15 na man essential, misali; Labender da Rose da Peppermint da Citrus. Sai dai ki tabbata kin narkar da man sosai a cikin ruwan da zakiyi wankan dashi.

Matakan Da Zakibi Sune:

  • Zaki samu babban kwano koh kuma babban roba, sai ki hada dukkan gishirin da na lissafa a sama, bayan nan sai ki zuba bakar soda, sannan ki gaurayasu sosai, toh daga nan sai ki zuba man essential, idan kin yi hakan sai ki sake gaurayawa ya gaurayu sosai.
  • Zaki gauraya rabin kofin sinadaran da kika hada a 1 cikin ruwan da zakiyi wanka dashi, amma fa ba’a son kiyi wanka da ruwa mai sanyi da yawa, haka nan kuma ba’a son kiyi amfani da mai zafi sosai, kiyi amfani da ruwa mai dumi dai haka, so idan kina da bandaki na zamani, wanda akwai kwanon wanka wato (Baths) zaki iya cika shi da ruwa sannan ki zuba sinadaran 1 da yawa, idan kinyi hakan sai ki shiga ciki, a lokaci daya ki shafe kamar minti talatin koh kuma awa 1 a ciki, yin hakan zai kara wa fatarki haske da laushi da kuma taushi, sannan kuma zai kara miki kuzari sosai a jikinki.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*