
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
A yau in shaa Allahu zan waiwayi matan dake neman hanyar gyaran nonuwansu, kamar yanda muka sani a gyaran jiki, nono zai shiga a layin farko na mata, kasancewar sa babban alama dake iya bambanta mace da namiji kenan, kuma kamar yanda matar manzon rahma, Nana Aisha Allah Ya ƙara mata yarda ta ce, gemu ne adon maza, yayin da kuma nonuwa sune kwalliyar mata.
Toh kenan gyaran nono zai iya zama babbar kwalliya da ya kamata mata su sa a gaba fiye da kowacce irin kwalliya.
A wannan darasi zanyi bayani wa mata hanyar gyaran nono ta amfani da abu ɗaya, wato (tumfafiya) Kuma haɗi ne da bai tsaya a iya matan auren da suke shayarwa koh suka hayayyafa nonon ya zube ba, har ‘yan matan da suke fatan nononsu ya tsaya a yanda yake ba tare da ya zube ba za suyi Amfani dashi.
A wani vangaren kuma, wannan haɗin da nake shirin zayyanowa masu karatu magani ne ga wasu matsalolin nono, irinsu; ciwon nono (amma ba da ciwon da wasu daga manyan cutuka ke haifarwa ba, kamar ciwon daji da sauransu), sanyin nono da makarantan su.
Toh Kenan Ta Yaya Za’a Hada Wannan Hadin?
Da farko zaki nemo ƙwallon tumfafiya, ba tare da an fasashi ba, za’a shanya shi (kuma a guje wa yin abinda zai fashe kafin a shanya shi din), sai ya bushe sosai, kafin a daka shi ya koma gari.
Sannan za’a iya tankadewa, amma abinda yafi, sai an cire wani farin abu mai kama da kaɗa, wanda shi ba zai daku ba, sannan a nemo man shanu mai kyau wanda bashida Hadi, shima ɗanye wanda ba’a soya ba.
Sai a haɗa waɗannan abubuwan guda biyu a wuri daya, a cakuɗasu sosai, sai a samu mazubi mai marfi kuma mai kyau a saka, a rufe.
Zaki dinga shafawa akan nonuwanki, amma zai kasance kina murzawa tsayin lokaci, ba iya shafawa kadai ba, Abin nufi, idan kika shafa, zaki dinga sanya hannu kina matsawa, tamkar dai kina fatan ki shigar da maganin ga cikin fatar ba iya samanta ba kadai ba.
Wannan haɗin zai iya kara wa mace mai shayarwa ruwan nono, ya kuma ciko da nonuwan da suka zube, sannan ya tsayar da waɗanda ba su zube ba, ga uwa uba kuma maganin wasu daga cikin cututan nono da yakeyi kamar yanda na faɗa muku a baya.
Abin lura:
Sanin mu ne man shanu ɗanye na da ƙamshin da ba kowa ne yake sha’awar jinsa a jikinsa koh jikin matarshi ba, toh don haka yake da muhimmanci kafin kisa kisan lokutan da suka fi dacewa kiyi amfani da wannan daɗin, da kuma yanda zaki kula da jikinki bayan kin tabbatar haɗin ya gama shigewa a inda aka saka shi.
Ma’ana dai, ki tanadi turare na musamman don tabbatar da idan kin yi wanka zaki iya batar da warin man daga jikinki saboda gujewa matsala.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply