Yanda Ake Hada Hadadden Dilkan Gyaran Jiki Cikin Sauki:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

A yau ma na kawo muku yanda zakuyi hadin hadadden dilka na Amare wanda zai gyara miki Jiki, fatanki tayi kyau ki koma gwanin ban sha’awa.

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Ruwan lemon tsami.
  • Kwai.
  • Zuma.
  • Ruwan madara cokali 3.
  • Ruwan suga da kanwa kowace iri.
  • Ruwan Alif bayawa ba.
  • Man zaituun amma bada yawa ba.

Wadannan sune ruwan da ake hadin dilka dasu.

Saura kuma garin da ake hadawa.

  • Lallin gargajiya.
  • Garin ganyan magarya cokali 3.
  • Garin yalon kurkur da jan kurkur wato (Tumeric ).

Wadancan ruwayen dana tanada da farko, dasu za ahade su wuri guda a cakudasu sosai akuma tabbatar sun hade sosai da sosai, sannan wadannan garikan suma azuba su a cikin wannan hadadden ruwan adamesu sudamu sosai, amma in anga sunyi kauri da yawa toh ana iya kara ruwan Alif da suga da kanwar nan dan su danyi dai-dai.

Shikenan sai ashafama Amarya aduk inda akeson ashafa mata.

Bayan ‘yan mintuna kamar 30 sai a gogemata da man zaituun.

Daganan sai ayi wanka da dafanfan ganyan magarya sannan asa madarar turare mai kanshi irin wanda ake so.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*