Yanda Ake Hada Maganin Da yake Wanke Dattin Ciki Da Dattin Mara Maza Da Mata Cikin Sauki

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Za’a Samu Wadannan Abubuwa Guda 10 Dazan Lissafosu Wanda Dukansu Basuda Wahalar samu:

  1. Za’a Samu Asalin Ganyen Zaituun sai a dakashi ya dawo gari sosai, a kalla ana son cikin babban cokali 3.
  2. Sai Tsohuwar Tsamiya ba danyar ba, idan akace tsohuwar tsamiya itace wacce zaka ga tayi brown koh jah kuma ita tana da danko sosai itace tsohuwar tsamiya za’a samu guda 7.
  3. Sannan za’a samu Jan gauta wacce ta bushe kuma wacce bata dagargaje ba itama guda guda bakwai.
  4. Sai Lemun Tsami Guda bakwai shima amma mai kyau ba busashshe ba.
  5. Garin Sanamaki/Fulasko Shi Ana samunshi a Islamic chemist, anason a kalla yakai kimanin cokali 3 babban cokali.
  6. Sai Tafarnuwa mai kyau kwallo 3 kuma a bare busasshen bawonta a yayyanka ta kanana-kanana.
  7. Albasa Fara babba mai kyau guda 1 bajaba fara akeso.
  8. Dabino Mai kyau a kalla kamar guda ashirin a baresu a cire kwallon, a kuma cire Dattin ciki har wannan Leda-Ledar farin duk a cireshi.
  9. Ganyen Zogala busasshe kuma garin a kalla ya kai kamar cikin cokali 3 babban cokalin cin abinci.
  10. Sai Na Karshe Shine Zobo, zobo dai da aka sani wanda ake jikawa yayi jah a sa suga a sha shi nake nufi, a daka garinsa shima a kalla ya kai iamar cikin cokalin cin abinci 3.

Sannan sai a samu ruwa mai kyau a kalla ya kai kimanin Liter 2, koh 3, toh sannan sai a juye wadannan kayayyakin da na lissafo guda 10 din a cikin wani abu mai dan girma wanda zai dauke su, sai a barshi ya kwana tukunna a ciki sannan sai a juye a tukunya a dafa su su tafasa sai a tace azubashi a cikin wani mazubi Mai kyau wanda bazai lalata shi ba, sai a dinga sha bayan anci abinci kullum sau 2 a yini.

Ana son in aka ci abinci aka sha a tsaye sai a zauna a bubbude kafafuwa a saki jiki ana Numfashi sosai ta yanda mara da ciki zasu sakata su wala maganin ya ratsasu sosai tsawon mintuna 10 sai a cigaba da harkokin da aka saba na yau da kullum, da yamma ma a kara yin haka, in ana azumine kuma ana sha lokacin Sahur da lokacin bude baki (Iftihar) ana daukar kwana bakwai ne a cikin kowanne wata ana yin Service, in shaa Allahu dukkan Dattin dake cikin mara koh ciki koh kuma tsutsar ciki, koh rubabben maniyyin dake dankarewa a marar maza koh Rana koh kuma wani cuta wacce take mara koh ciki In shaa Allahu wannan maganin zai wankosu gabaki daya, zai dinga fitar dasu ta hanyar fitsari koh ta kashi wayo (bayangida) saidai kuma idan mutum yana da ulcer ana son in ya sha ya kara da ruwan sanyi in shaa Allahu ulcer din baza ta tashi mishi ba.

Sannan wannan maganin ba iya dattin ciki da mara kadai yake magancewa ba, yana wanko Har dattin da kan zama barazana ga hunhu koh hanta koh kuma koda, sannan yana wanko mahaifa ga mata kuma yana wanke Jijiyoyin azzakari na da namiji, kuma mace mai ciki zata iya amfani da wannan magani ba bazai bata matsala ba in shaa Allahu, kuma ana iya bawa yara kanana amma yanda zasu sha dai-dai yanda zai dauki cikinsu ne, ya danganta da shekaru koh girman yaron.

Wato idan namiji koh mace babba baligi koh baliga zai sha cikin karamin kofi toh wanda bai Balaga ba indai yana iya cin abinci zai sha rabin karamin kofi kenan shi, amma idan yaron bai fara cin abinci ba ba a bashi, domin ana sha ne bayan an ci abinci an koshi, Allah yasa mu dace.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*