
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
A yau duba da irin tambayoyin da wasu keyi min suna neman shawara na idan zasuyi sabon aure, yasa na kawo muku wannan bayani akan yanda ake hada kazar amare kashi na Farko.
Wannan hadin hadi ne na musamman wanda zai karawa mace ni’ima sannan kuma ya zauna a cikin jikinta harna tsawon wata uku ba tare da ya salamce ba, ina nufin idan mace tayi wannan hadin bazata kara yin shi basai bayan tayi wata 3 sannan zata Kuma yin wani.
Abubuwan Buƙata Sune:
- Kaza wanda bata fara kwai ba
- Ridi
- Nonon Rakumi
Yanda Za’a Hada:
Za’a yanka kazar sannan a zare kayan cikin ba tare da an yanka ta kanana ba, sai a gyara ridi a sanyashi ya bushe sai a daka shi, a hada ridin da nonon rakumi a zuba cikin kazar sai a daure zumbutun a saka ta a cikin kayan miya a dinga dafa ta har saita dahu lubus sannan ki sauke.
Saiki sake a plate koh kula koh kwano ki cinye Abinki.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply