
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com
Yau na kawo muku yanda zakuyi hadadden hadin garin sha’ir domin motso da sha’awa, karin ni’ima da samun Dandano fiyeda yanda ake tsammani ga ma’aurata.
Abubuwan Da Zaki Buƙata Sune:
- Garin sha’ir
- Garin alkama
- Garin dabino
- Garin farar shinkafa wato (Shinkafar tuwo)
- Nonon akuya
Dafarko zaki samu wadannan kayayyakin hadin sai ki hadesu guri daya ki gauraya ki dinga sha da nonon akuya.
Yadda Zaki Hadin Sassaken Baure Domin Karin Ni’ima:
Zaki Samu Wadannan Kayan:
- Sassaken baure
- Garin kanunfari
- Mazarkwaila
- Garin citta
- Garin minannas
- Zuma
Idan kika samu sassaken baure kika tafasa bayan ya tafasa sai ki sauke ki tace sai ruwan ki maidashi kan wuta sannan ki zuba sauran kayan hadin ki dafa sosai sai ki sauke ki kara tacewa ki maida shi ruwan shanki.
Yadda Zaki Hadin Lubba Zakari Domin Rage Kiba:
Abubuwan Buƙata:
- Lubba zakari
- Garin Ganyen shayi Dan awo
- Garin habbatus sauda
- Suga
- Zuma
Zaki samu wadannan kayayyakin hadin ki hadesu guri day ki tafasa ki tace ruwan ki sa mishi suga ki kuma zuba mishi zuma a ciki saiki juya ki dinga diba kina sha, in shaa Allahu kiban zai rage.
Yadda Ake Yin Hadin Kyauta Bashiri:
‘Yar uwa wannan hadin yana da matukar muhimmanci domin yana saurin saukar da ni’ima kuma yana sa mai gida yaji wani dandano na musamman wanda Bai saba jin irinsaba.
Abubuwan Buƙata Sune:
- Kokomba
- Tuffa wato (Apple)
- Garin albabunaj
- Garin citta
- Madara peak ta ruwa
Zaki samu kokombanki mai kyau ki yankata kanana-kanana sai tuffanki itama ki yanka sai ki hadasu ki markada sai ki zuba garin citta da garin albabunaj sannan ki juya ki barshi ya jiku saiki tace ki zuba madara sai ki dinga sha tundaga rana har dare.
Don Allah a turawa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply