
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
A yau ma na kawo muku yanda zakuyi hallaka Kwabo mai dadi kuma Mai saukin hadawa wanda bazakisha wahalar yinshi ba.
Abubuwan Buƙata Sune:
- Gyada
- Suga
- Butter
Dafarko zaki samu karamar tukunya koh karamin kaskon suya sai ki dora a wuta sannan ki dauko butter ki zuba kamar cikin babban cokali daya, bayan ta narke saiki dauko sugar kamar gwangwani daya koh 2 (adadin yawan gyadar da zata hada din, misali idan gyadar gwangwani biyu ce toh sai kisa sugar din gwangwani 1 ya isa), sai ki zuba a cikin butter din ki barshi ya narke sosai toh kada ki sauke da wuri.
Toh daga nan sai ki dauko gyadar amma anfi son wacce aka soya marar bawo koh ba’a soya bama ba matsala sai a juye a kwano mai karfi koh a zuba a karamin turmi sai a dan daddaka sama-sama sannan a kwashe a ajiye.
Toh daga nan saiki koma kan wannan sugar da butter din dake kan wuta sai kici gaba da juyawa yana dahuwa har sai ya canja kala sosai ya zama kalar (coffee) sannan ki dan saka cokali ki debo kadan sai ki zuba a faranti bayan minti daya zaki ga ya bushe yayi tauri sosai toh hakan alamar hadin ya dahu kenan, toh sai ki dauko wannan gyadar ki juye a cikin sugan dake kan wuta saiki cakuda sosai bayan mintuna 2 koh 3 sai ki sauke amma kina saukewa saiki juye a faranti mai fadi babba.
Bayan kin juye a farantin ya dan sha iska sai ki dauko wuka ki yayyanka gida-gida dai-dai girman da kike bukata sannan sai ki banbare daga farantin kada ya kame ajiki ki rarraba su a hankali.
Ga Kuma Hanya Ta Biyu
A wannan bangaren ba a amfani da butter kawai zaki daura tukunya a wuta ne sai ki dauko sugar ki zuba ki barshi ya narke saiki dauko gyadar ki daka ta sosai tayi laushi ba kamar a hadin farko da zaki daka sama-sama ba a wannan karon gyadar sai tayi laushi sosai sannan saiki sauke wannan sugar dakika dafa sai ki dauko wannan garin gyadar ki zuba a ciki sai ki rinka tukawa kamar tukin tuwo sai ya hadu sosai amma kada gyadar tayiwa sugar din yawa toh saiki mayar kan wuta bayan minti daya ki sauke.
Amma banbancin su kawai shine hadin farko ba’a daka gyadar gaba daya sannan ana zuba butter kafin a zuba sugar wanda wannan butter din tana karawa hadin kyau da santsi saboda gyadar da ba’a daka sosai ba wannan butter zata taimaka wajen dai-dai ta laushin sa idan ana ci a baki.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply