Yanda Ake Hadin Halawa Da Yanda Ake Shafata Ajiki Domin Gyaran Jiki Da Gyaran Amare:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com

A yau in shaa Allahu zan koya muku yanda zaku harhada kayan gyaran jiki na amare.

Bari na tafi kai tsaye na fara da yanda zaki hada halawa ta gyaran jikin amare.

Yanda Zaki Hada Hadawa:

  • Sugar ko xuma
  • Lemon tsami
  • Ruwa

Yanda zaki hada kuwa shine, zaki dora suga a kan wuta amma karki cika masa wuta sosai saboda karya kone, zaki barshi har sai ya narke sai ki matse lemun tsami a ciki tare da dan ruwa kadan saiki bari ya dahu ya hade jikinsa ya koma Brown colour sosai sai ki sauke ki bari ya huce sannan ki rinka diba kina mannawa a jikin ki kina dayewa toh da zarar kina yin wannan jikin ki zaiyi kyau fatarki zata goge tayi santsi da shining kuma zai fitar miki da duk wasu kanan gashi da gishirin fuska da duk wasu abubuwan da suke hana fuska tayi subul duk zai cire miki su.

Toh bayan kuma kinyi wannan sai ki hada kurkum mai kayan hadi na amare ki shafashi, shima wannan hadin na kurkum in shaa Allahu wani satin zan koya muku yanda akeyinshi, kusani ni kullum burina naganku yan uwana kun gyaru sosai kun zama taurari a gun mai house, sannan kuma wannan hadin basai amarya ba uwar gida ma zatayi domin yana sawa ki koma tamkar jarirya fatarki tayi laushi da santsi kiyi kyau sosai Abinki.

Yanda Zaki Hada Halawa Domin Samun Santsin Fatarki:

Ana yin hadin halawa domin samun sulbin fata koh kuma ga matan da suke fama da gashin jiki kamar a hannuwa da kafafuwansu.

Sannan kuma anayin hadin halawa ne domin samun sulbin fata koh kuma ga matan da suke fama da gashin jiki kamar a hannuwa da kafafuwa, kuma halawa ta samo usuli ne daga mutanen borno, wannan na daya daga cikin al’adunsu na gyara amaryar gobe kafin ayi mata rufi, toh amma a yanzu zamani ya canja inda har wasu kabilun ke amfani dashi ga amaren gobe koh don gyaran fata, kowace mace akwai irin ababen da take hadawa wajen yin hadin nata halawar, sannan ni ma na kawo muku irin nawa yanayin hadin, ku kasance wajen yin halawa kamar sau 1 a wata domin samun fata mai santsi da laushi da kuma rabuwa da gashin fata.

Abubuwan Da Zaki Buƙata:

  • Cokula 3 na sukari
  • Lemun tsami guda 3
  • Ruwa cokali 1.

Yanda Zaki Hada:

Zaki zuba suga a tukunya mai zafi, idan ya fara narkewa sai ki zuba ruwan lemun tsami da ruwa kadan, ki tabbatar cewa wutar ba mai yawa bace wanda aka daura halawar a kai saboda kada ya kone, kiyi ta juyawa har na tsawon minti arba’in da biyar har sai hadin ya koma ruwan kasa sannan ki sauke daga kan wuta, saiki jira ya huce, zakiga yayi danko, saiki samu cokalin katako koh na roba ki shafa a kan fata inda ke da gashin, sai bayan ya bushe, sannan ki samu tsumma ki danna a kan fatan saiki rinka ciro shi, yin hakan na fitar da gashin fata kuma zakiga fatar tayi sulbi da santsi.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*