
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
Wani abin ban mamaki tasirin tsumin mallaka da akeyi da ‘ya’yan itatuwa a halin yanzu ya kankama, domin har yau bai samu tsaraba ta fuskar gamsar da miji bawai ina nufin yafi kowanne tsumi samar da ni’ima bane.
Shi wannan tsumin bazai yuwu kisha mijinki baiji dadin kwanciya dakeba saboda yana daya daga cikin maganin mallakar miji mai bukata, mun dade muna bincike akansa kafin mu tabbatar da ingancinsa shiyasa akeson mai wannan hadin ya zamana tanada fridge domin ajiyar sa don mace anason tasha safe da yamma musamman idan mijinta yana nan wannan kenan.
Shi tsumin da akeyi da goron tula ba kuma irin wanda kuka saba gani ana saka goron tula daya a liter uku na ruwa bane, shi wannan hadin tsumine na musamman wanda akeson asamu goron tula akalla guda biyar, sannan kuma a samu sassaken baure kadan sai asuwakin mata kamar guda uku, sai garin dan bashanana cokali 2, sai kuma garin ‘ya’yan kargo Shima cokali 2, sannan da ganyen idon zakara cokali 5, wadannan sun isheki sai kuma yanda ake dafawa.
Zaki fara bare goron tula din sannan saiki saka itatuwan da ganyen amma banda garin, saiki wankesu sannan ki zuba musu ruwa kamar liter daya da rabi sannan saiki zuba sauran garin ki tafasa idan ya tafasa ki tace ruwan saiki ajiyesu don zaki iya sake dafawa amma a karo na 2 ruwan kada ya wuce liter daya, bayan kin tace saiki saka mazarkwaila koh kuma zuma.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply