Yanda Zaki Amfani Da Aloe Vera Wajen Gyaran Fata:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com

Akwai mata da dama da suke sha’awar ganin fatarsu ta yi subul-subul babu ƙuraje koh kaɗan, wadannan ganyen yana ɗauke ne da sinadarai da dama waɗanda sukan iya kara tsawon gashin kan mace, sannan yikan aanya fuska tayi sheƙi da gyaran jiki dadai sauransu, saboda haka ne a yau na kawo muku hanyoyin da zakubi kuyi amfani da ganyen wajen gyaran fata da kuma gashin kai, inaso masu karatu ku gane cewa a duk rubutun da nake yi, idan na lissafo ababen hadin kwalliya, guda 1 daga ciki nake so a rinka amfani dashi domin yawan sanya wa fuska ababe da dama na haifar da fesowar ƙuraje.

Abubuwan Da Yakeyi:

  1. Koɗewar fuska: yawan aiki koh kuma shiga rana yana sanya fuska ta yi baƙi koh kuma launinta ya zama biyu, toh a samu ganyen ‘aloe bera’ a matse ruwan sai a matsa ruwan lemun tsami sannan a kwaba a rinka shafawa a fuska domin gyaran irin wannan fatar.
  2. Yanƙwashewar fata: shi wannan ganyen yana rage shekaru daga fuskar mutum, za’a matse ruwan sa sannan a haɗa da ruwan (rose) sannan a rinka shafawa a fuska a barshi yayi harna tsawon minti 10 zuwa minti 15 kafin a wanke a kullum.
  3. Domin fuska mai yawan gumi koh maiko: za’a samu ganyen aloe vera sai a dan kankare bayansa sannan a ɗora a tukunya da ruwa a ciki har sai yayi laushi sannan a sauke a zuba zuma a ciki, bayan ya huce sai a shafa a fuska harna tsawon minti ashirin a kullum kafin a shiga wanka.
  4. Domin gautsin fata: shi kuma za’a markaɗe dabino da gurji sannan a matse ruwan ganyen aloe veran da ruwan lemun tsami sai a shafa a fuska da jiki gaba daya harna tsawon minti 30 kafin a wanke.
  5. Gyaran gashi: Shi kuma matse ruwan aloe beran za’ayi sannan a haɗa da man zaituun a kwaɓasu su kwaɓu sosai sannan a rinka shafawa a fatar kai da kuma saman gashin a duk lokacin da aka yi niyyar wanke gashin kai kafin a wanke, shi kuma yin hakan yana sanya baƙin gashi da kuma daɗa wa gashin tsawo da ƙarfi da yardar Allah.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*