
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
A yauma in shaa Allahu zan kawo muku yanda zaku hada hadadden maganin da zai fatattaki Ciwon sanyi cikin sauki, da izinin Allah.
Idan mace tana fama da kaikayi koh kuma kuraje koh fitar farin ruwa mai wari koh bushewa koh daukewar ni’ima koh budewar gaba da kwailewa da rashin sha’awa koh gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, toh ta gwada daya daga cikin wadannan hanyoyin da zan kawo yanzu in shaa Allahu za’a samu waraka.
- Za’a samu saiwar garafuni da sassaken nagarya, sai a tafasa, idan an tafasa ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa dashi, a kullum sau daya, yin hakan yana maganin budewar gaba da kuma kaikayi.
- Sannan kuma za’a samu garafuni da sassaken sanya sai a tafasa, sai mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi kuma da yamma, shikuma yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari da yake fita a gaban mace.
- Za’a samu furen tumfafiya, sai a shanya ya bushe, idan ya bushe sai a daka a dinga zubawa a cikin nono ana sha, shi kuma yana magance matsalar ruwan infection.
- Za’a samu lalli da ganyen magarya da kaninfari, a hadasu waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki, idan ya dan huce sai a shiga ciki a zauna na tsawon kamar minti 10 yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.
- Har ila yau kuma za’a samu kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsameta daga ruwa a jajjagata koh a birga, a zuba madara koh Nono sannan a sa zuma a sha, wannan kuma yana mganin rashin sha’awa da bushewar gaba da rashin gamsuwa yayin jima’i.
- Za’a dafa zogala, idan ya dahu sai a murje shi koh a dama, a tace, ayi lemun juice da shi, yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni’ima sosai.
- Za kuma a samu `dan-tamburawa da albabunaj a tafasa a zuba man hulba a ciki, sai a dan tsuguna tururin ya dinga shiga cikin gabanki, I kuma ya dan huce sai a shiga ciki a zauna, yin hakan zai magance maki kaikayi da kuraje sannan kuma yana sa mace ta matse.
- Za’a samu farin Albasa da Kaninfari da citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai a dake su ayi Yaji a dinga cin abinci da shi, yin hakan na saukar da ni’ima da magance duk wasu matsalolin sanyi.
- Za’a samu Sabulun Zaituun da Sabulun Habbatusswaudah sai a daka su, a samu ganyen magarya da garin Bagaruwa a daka a tankade, sannan sai a zuba akan sabulan da aka daka a kwa6a da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski, sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau 1, da ruwan dumi amma ake tsarki da shi, wannan sabulu yana maganin kuraje da kaikayi da fitar da warin gaba.
- Za’a samu man Zaituun da Man Habbatusswaudah da Man Tafarnuwa da Man Kaninfari sai a hadasu waje daya, mace ta dinga shan cokali 1 kullum kafin ta karya, yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni’ima sosai.
- Sannan kuma za’a samu ciyawar Kashe-zaki da farin magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali tana sha, sannan ta dinga shan Man Zaituun Cokali 1 kullum kafin ta karya, wannan yana maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.
Illolin Da Ciwon Sanyi Yakeyiwa Mata:
- Yana saka rashin sha’awa.
- Yana sa ciwon mara mai tsananin gaske.
- Yana haifar da kurajen bakin mahaifa koh ya toshe mahaifar ma baki daya.
- Sannan kuma yana sa mace ta dinga jinin al’ada bakinkirin kuma mai wari.
- Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fitowa mace ta gabanta.
- Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta warin bazai bata ba.
- Kuma yana sa jin zafi yayin saduwar aure koh kuma ganin jini a maimakon ruwa.
- Sannan kuma yana rikitarwa mace kwanakin al’adarta, su dinga karuwa koh raguwa koh jinin ya dinga wasa.
- Sannan kuma yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ya dinga fita ta gabanta.
- Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki koh kuma rashin shigar cikinma kwata-kwata.
- Idan kuma yayi karfi toh yana hana mace haihuwa.
- Wani infection din Kuma alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare koh kuma jarirai.
Amma Abin Lura Anan Shine:
Idan mace tayi magungunan asibiti da kuma irin wadannan da mu ka ambata amma infection din bai warke ba, toh ta nemi maganin jinnul ashik, wato magungunan Aljanu don zai iya yiwuwa matsalarsu ce.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply