Yanda Zaki Hada Sabulun Zuma Don Gyaran Jiki Da Fidda Kowanne Irin Tabo Cikin Sauki

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Yanda zaku hada sabulun gyaran Jiki mai kyau a cikin gidanku

Yana da kyau mata su san yanda ake hada irin wadannan sabulun domin gyaran jiki koh kuma don yin sana’a.

Yawan shafe-shafe yana bata fatar jiki don haka idan ana shafa abu kadan a fatar jiki, yafi amfani da kuma gyaran fata, toh a yau na kawo muku hanyoyi daban-daban wa’inda za a yi amfani da sabulun salo don gyaran fata.

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Sabulun salo
  • Zuma
  • Bitamin E
  • Man almond (za’a iya samun sa a shagunan masu saida kayan kwalliya)

Yanda Za’a Hada:

Za’a daka sabulun salon koh kuma a saka abin kankare kubewa a kankare, sannan sai a zuba ruwa domin ya narkar da sabulun, sannan sai a zuba ‘bitamin E’ da man ‘almond’ sai a kwabasu sosai, irin wannan hadin na gyara fatar jiki da kuma sanya fata tayi subul-subul da laushi.

Ga Kuma Hadi Na Biyu:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Sabulun salo
  • Man kadanya
  • Ruwan ganyen ‘aloe vera’

Yanda Za’a Hada:

Za’a narka man kadanya da ruwan zafi sannan a narkar da sabulun salon shima, sai a samu gora a zuba hadin man kaden tare da na man kadanya da ruwan ganyen ‘aloe vera’ sannan a girgiza su domin su hadu sosai.

Amma za’a iya amfani da shi nan take daga gama hadawa koh kuma a zuba a bar shi tsawon sati biyu sannan a fara amfani dashi.

Ga Hadi na Uku:

Abubuwan Buƙata Sune:

  • Sabulun salo
  • Zuma
  • Kurkum
  • Man kwakwa
  • Man Zaituun

Yanda Za’a Hada:

Bayan an narkar da sabulun salo a ruwan zafi, sai a zuba zuma da kurkum da man kwa-kwa da kuma man zaituun, a zuba su a cikin gora sannan a girgiza sosai domin su hadu sosai, sai a zuba a murta.

Za’a iya amfani da wannan hadin nan take koh kuma a jira yayi tauri bayan sati biyu sannan a fara amfani da shi.

Wannan hadin Shima yana magance kuraje, gumi koh na fuska da wasu cututtukan fata.

Yanda za’a magance matsalan tabo a Jiki Akwai hanyoyi da dama wanda za’a bi don magance tabo a fata amma a yau na kawo muku hanyoyi masu sauki domin magance tabo a fata, idan tabo ya yi yawa a fatar mace, yana boye kyawunta, don haka ya kamata a kula da fatar jiki sosai.

Ga Wasu Abubuwa Guda Uku Da Za’ayi Amfani Dasu Domin Magance Tabo A Fata Kamar Haka:

  1. Kurkum: Za’a samu kurkum sai a hada shi da madarar ruwa yanda zaiyi kauri sannan a shafa a kan tabo, sai a barshi yayi kamar tsawon minti 5 zuwa 10 sannan a wanke.

Za’a cigaba da shafa wannan hadin sau 2 a rana kamar tsawon watanni 3 koh 4.

  1. Lemun tsami: Za’a yanka lemun tsami gida 2 sannan a yaryada masa siga sannan a dirza shi a kan tabon na tsawon minti 5.
  2. Ganyen ‘Aloe vera’: Shima za’a matse ruwan dake cikin ganyen ‘aloe vera’ sannan a shafa a tabo na tsawon lokutan da za’a iya bari, sannan sai a wanke, a rinka yin hakan kamar sau 2 koh 3 a rana, sannan kuma za’a iya ci gaba da yin hakan har na tsawon watanni 3.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*