Yanda Zaki Hada Sahihin Maganin Rage Kiba Koh Tumbi Cikin Kankanin Lokaci Maza Da Mata:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com

A yau in shaa Allahu zan kawo muku yanda zakuyi ku hada maganin da zai rage muku kiba koh kuma tumbi cikin sauki Kuma yayi muku aiki da yardar Allah, sannan kuma wannan hadin maganin ba iya mata kadai zasuyi amfani dashi ba, har Maza ma zasu iya amfani dashi idan dai har suna buƙata.

Yanda Zaku Hada Maganin Kuwa Shine:

Zaku samu danyar citta guda 2 masu kyau saiki yayyankashi koh ki dandakashi, daganan sai ki samu lemun tsami shima guda 1 ki matsa ki hadasu duka ki tafasa da ruwa cikin kofi 1 idan ya tafasa saiki tace.

Yanda Ake Sha:

Zaki dinga shan wannnan hadin sau 2 a rana harna tsawon sati 2 wato mako biyu, toh kuwa in shaa Allahu idan kukai wannan hadin zakusha mamaki da izinin Allah.

Ga Wani Dan Takaitaccen Karin Bayani Akan Maganin:

Duk wanda keson ya rage kiba da nauyi toh yakamata yasani cewa dole ne sai ya canza yanayin cin abinci da kuma yanayin yanda mutum yake gudanar da rayuwarshi gaskiya.

  • Sai ya rage cin abinci mai kitse wato (fat)
  • Sannan ya dinga yawan motsa jikinshi wato (Exercise)
  • A dinnga cin ganyayyaki da kayan marmari wato (fruits)
  • Dole ne arage yawan zama ana kallon tv koh kuma yawan danna computer
  • Sannan bada tazarar awa 2 idan akaci abincin dare kafin a kwanta barci.

Ga Wani Dan Gargadi Dazanyi:

Idan har mace tanada yaron ciki watoh Juna biyu karami koh kuma masu fama da ulcer irin mai tsanani dinnan toh dolene su nisanci amfani da wannan hadin maganin.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*