Yanda Zaki Hadadden Waina (Masa) Tayi Kyau Tayi Tashi Cikin Sauki:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

A yau in shaa Allahu zan kawo muku yanda zakuyi Wainar shinkafa zatayi kyau tayi tashi fiyeda yanda kike zato, zatayi gwanin ban sha’awa wanda idan mutum yagani koh bai cin waina sai yaci saboda kyawunshi.

Abubuwan Da Zaki Buƙata:

  • Shinkafar tuwo (farar shinkafa)
  • Yis
  • Bakar hoda
  • Suga
  • Kanwa wato ungurnu

Yanda Zaki Hada:

Da farko dai zaki soma wanke shinkafarki tawanku sosai, tayi tas ki bayar amarkado miki bawai saita jiƙu ba, a’a dakin wanke kibada akai a markaɗa miki, idan amkawo miki sai ki zuba yis da Bakar hoda kadan sai kisa suga idan kinaso, sai kirufe kikai rana, idan yatashi sai ki dauko kizuba dafaffiyar shinkafa data nuna duk da dai wasu kafin amarkado musu suke zuba dafaffiyar shinkafar sai amarkado da danyar, wasu kuma sai anmarkado suke zubawa yadanganta da yanda mutum yake ra ayinsa, bayan haka sai kizuba ruwan kanwa kadan kijuya ki fara soyawa atanda idantayi ja sai ki kwashe.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*