
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
Mafi yawancin mutane musamman mata suna sha’awar farar fata, so da yawa zaka tarar masu farar fatar ma na son kara wa fatarsu haske, kuma garin hakan sai kiga sun sanya fatarsu cikin rudani wato abinda hausawa ke cewa ‘garin gyaran gira sai a rasa ido’.
Da akwai wasu hanyoyi da dama daya kamata a bi wajen karama fata haske, za iya hakan ne ta hanyar amfani da nau’o’in mai na zamani dadai sauransu.
Sannan kuma zafin rana kan kodar da fata kasancewar tana dauke da zafin ‘Ultra biolet rays’, a lokaci daya gumi da kura da kuma yawan shekaru na sanya fata dafewa, sinadarin melanin dake jikin fata ne yake haifar da baki musamman ma idan ya yi yawa a jikin mutum, shi sinadarin ‘melanin’ yana kare fata daga wahalhalu, shiyasa sauda dama fararen mata sunfi samun yawan laulayi.
Dukan maya-mayun dasuke kara hasken fuska toh suna dauke da sinadarin rage ‘melanin’ daga fata, aloe vera da lemon tsami yana rage bakin dake jikin fata, sannan banda su gama wasu hanyoyin da za’a samu farar fata sosai.
Yanda zakuyi amfani da ’ya’yan itace don rage bakin dake jikin fata ayi haske ba mai cutarwa ba
Dafarko zaki iya bare bawon lemun zaki sai ki busar dashi wato ki shanyashi a rana, idan yabushe, sai ki nika, sannan ki hada da nono koh ( madara), daga nan sai ki kwaba, ki rinka shafawa a jikinki safe da yamma, sannan duk sanda kika shafa bayan ya Dauki dan lokaci sai ki wanke da ruwan dumi, shi wannan zai kara wa fatarki haske sosan gaske.
Ga wata hanyar itama ta yin fari wato haske, zaKi iya neman itacen sandal wood wanda ake turaren wuta dashi, saiki hada da shi a hodar sandal wood din, daganan saiki kwaba sosai, sannan sai ki rinka shafawa sau 2 a rana, safe da yamma shima, ki bar hadin ya bushe, bayan tsawon lokaci saiki wanke domin hakan zai sanya fatarki ta yi hasken da bakiyi tsammani ba in shaa Allah.
Wata hanyar yin hasken kuma wanda yakamata kusani shine, amfani da dankalin turawa shima yana da sinadarin kara hasken fata, zaki iya markada shi, saiki rinka shafawa kafin ki kwanta barci, wannan hadin shi ma yana taimakawa wajen kara wa fata haske sosai.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply