Yanda Zaki Tsiren Tukunya Cikin Sauki Kina Zaune A Cikin Gidanki:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com

A yau in shaa Allahu zan kawo muku yanda zakuyi tsiren tukunya a cikin gidajenku Kuna daga zaune abinku kuma cikin Sauki.

Abubuwan Da Zaki Buƙata:

  • Jan nama
  • Albasa
  • Maggi
  • Yaji
  • Kulkuli
  • Kayan kamshi
  • Man gyada
  • Koren tattasai

Yanda Zaki Hada:

Toh dafarko dai zaki wanke namanki kiyi mishi yanka mai fadi-fadi, saiki ajiye a gefe, bayan kin ajiye a gefe daban, sannan saiki hada yaji da mangyada da garin kulkuli kisa mishi maggi da kayan kamshi saiki kwaba, bayan kin kwaba saiki dinga shafawa a jikin naman gaba da baya, Idan kingama saiki kawo tukunyarki marar kamawa saiki jera a ciki kidorashi a wuta kirufe ki barshi karkisa wutar tayi yawa saboda idan wuta yayi yawa zaisa Naman ya kone, toh daga nan saiki dinga juyawa idan yayi saiki sauke ki yanka daidai misali kisa a plate sannan kiyanka albasa da koren tattasai kanana-kanana.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*