Yanda Zakisa Mijinki Ya Kaunaceki Fiyeda Yanda Kike Tunani A Zuciyar Sa:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Da akwai dabaru da hikimomi, hadi da kissa da kuma kisisina masu tarin yawa da mace zata iya amfani dasu domin ganin ta cusawa mijinta kaunarta acikin zuciyarsa, irin wadannan dabaru ba wani wuya koh wahalar gudanar wa suke dashi ba, sai dai mata da dama basa iya aiwatar da irin wadannan dabarun, ga wasu dabaru na yanda zaki jawo soyayar mijinki cikin sauki dazan kawo muku.

  1. Yin wanka tare: ba duka matane sukasan cewa yin wanka tare da miji yana kara dankon soyayya ba, koda kuwa ke baza kiyi ba, toh kiyi kokarin ganin kin cuda shi kin wankeshi tas kafin shi ya daureye kansa, wannan salon dabaran mallakar miji yana da tasiri matuka ga duk macen da zata saba yiwa mijinta hakan gaskiya.
  2. Yin girki na musamman: yiwa namiji girki na nusamman da kikasan yana so shima wani salo ne na mallakar miji cikin sauki, kada kiji kyashin kashe abunda yafi abinda ya baki na hada wannan abincin, duk macen da zata yi amfani da wannan dabaran na girki zata cusawa mijinta kaunarta a cikin zuciyarshi cikin sauki wallahi.
  3. Cin abinci Tare dashi: cin abinci Tare da mijinki shima wani salo ne na mallakar miji, koda miji yana cin abinci da abokai koh ‘yan uwane, ki rinka samun wani abinci koh kayan kwalama na musamman da zaki rika bashi a lokacin da kuke ku biyu kuci tare.
  4. Yin gaisuwa cikin ladabi da biyayya: ki zamo mace mai gaida mijinta cikin ladabi duk safiya idan kun tashi, haka kuma ki zama mai masa maraba cikin kauna idan ya dawo daga aiki, sannan kuma ki kasance mai masa fatan alkhairi a lokacin da zai fita nema koh ko Kuma waje aiki.
  5. Kada ki zama mai Mita: saboda yawan mita ga miji yakansa nan take ki fita daga cikin zuciyar namiji.
  6. Ki zamo mace mai barin magana a nan inda aka yita, ba tare da kinci gaba da mita akan abinda ya wuce ba.
  7. Kada ki zama mai zafin kishi: saboda wasu matan na dauka cewan idan suka nunawa namiji zafin kishi zai sa ya sosune, wanda sam ba haka bane, mata masu zafin kishi akasarin su suna rasa aurensu saboda wannan kishin nasu.
  8. Ki zamo mai nuna kishinki dai-dai gwargwado, wanda yin hakan zaisa shi mijin zai rinka gudun yin duk wani abinda zai saki kiji kishi akai.
  9. Toh amma idan kin zama mai zafin kishi a kullum zaki rinka samun matsala da mijinki, ta yanda hakan zaisa ki kasa samun soyayar sa kamar yanda ya kamata.
  10. Sannan babu ruwanki da duba wayarsa: mata da dama sun rasa mazansu saboda mugun halinsu na binciken wayar mazajensu, rashin daukar wayar miji wani dabara ne na mallakar mijinki cikin sauki amma ba dukannin matane suka san wannan sirrin ba.
  11. Kiyi kokari wajen gamsar da Miji: kada ki gaza wajen gamsar da mijinki a duk lokacin da yake bukatarki, gamsar da miji nasa miji ya kasance yana matukar kaunar matarsa yana kuma fata da burin ganin yayi rayuwarsa da ita har abada.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*