
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
Wannan hadin yana karawa mace ruwa da namiji ma baki daya.
Dafarko Zaki Samu Wadannan Abubuwan Kamar Haka:
- Kankana.
- Kokomba.
- Tumatir.
- Mazarkwaila.
- Madara Peak.
- Dabino.
Za’a yanka kankana duka a hada da ‘ya’yanta, ita ma kokonban duka za’a yankan harda bayan, kada a cire ‘ya’yan ta, a yanka tumatir shima kada a matse ruwan cikinsa sai a daka kaninfari a jika dabinon, sannan a cire kwallayen sai a hade su wuri daya, a marka dashi a blander, sai ki juye ki saka mazar kwailan ya narke sai a zuba zuma a juye madaran peak guda daya.
A rinka sha safe da yamma zaki sha mamaki uwargida hakama maigida zaisha mamaki Indai har kukayi wannan hadin toh lallai saikun godemin.
Har illah yau wadannan abubuwan suna da kyau mata su rinka amfani da su domin Karin Ni’ima da kuma samun wadataccen lafiya a jikinsu.
- Ruwan abarba: Yana da kyau mace ta rinka markadawa tana tacewa tana sha da suga koh zuma, wannan hadin yana karawa mace Ni’ima sosai fiyeda yanda take zato.
- Rake: Shima rake yana karawa mace ni’ima kuma yana da amfani matuka a jiki, domin yana karawa mata ruwa.
- Aya: itama aya duk tafiyar su daya da rake, ayar anason irin manyan nan tana da matukar muhimmanci gurin mace domin tana dauke da ni’ima sosai, kuma za’a iya samun kunun aya a hada shi da madarar peak ta ruwa a rinka sha.
- Zaituun: man zaituun yana magunguna da yawa toh shima anason mace ta rinka shafashi ajikinta hakan yana gyara fata da saka santsin jiki, hakama yanada kyau mace ta dinga shafawa a gabanta, yana saka laushin farji.
- Bawon bagaruwa: Ita kuma wani sirri ne wanda idan mace na son ta zama kullum a tsuke ta dinga dafa bawon tana shiga kamar yanda ake shiga ruwan dumi idan an haihu.
- Ga kuma wani hadin a nemi sassaken baure, kaninfari, zuma, citta, mazarkwaila, zaki tafasa sassaken baure ya dahu sosai saiki daka kaninfari mai yawa da citta yar kadan ki zuba akai, ki saka mazarkwailan da zuma amma zaki cire iccen kafin ki zuba hadin, sai ki sauke ki dinga sha dai-dai kima idan ya huce, wannan hadin kadai ya ishi mace, basai ta wahalar da kanta wajen neman boka koh wani asiri tana raba kanta da Allah ba.
- Sannan a samu zogala a wanke shi a nika shi tare da dabino da kuma kwakwa sai a tace a saka zuma tare da madara sannan a saka ya yi sanyi a rinka sha bayan sallahr mangariba.
- Shima wannan hadin yana kara ruwa, zaki samu ruwan kwakwa, nikakken ridi, garin dabino, madara ta ruwa a hadasu guri daya a dama miji zai sha mata ma zata sha.
- Sannan kuma ina mata masu fama da matsalar bushewar gaba? Toh ki samu man ridi ki rinka zubawa a cikin ruwan dumi ki zauna a ciki, sannan ki rinka matsi da albabunaj koh man hulba.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply