Yanda Zakiyi Tsumin Rake Mai Saukar Da Ni’ima, Tsumin Emergency Na Manyan Mata:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Yauma na kawo muku yanda zakuyi tsumin rake cikin Sauki ya Saukar miki da ni’ima sannan yayi miki hadin emergency na gaggawa.

Dafarko zaki yiyyanka rakenki kanana-kanana kamar alewar yara sai ki saka a tukunya da ruwa ki jefa kaninfari bada yawa ba fa da yar cittarki itama ba mai yawa ba sannan saiki bare dabinon ki kicire kwallayen ki jefar saiki dakashi ya zama gari saiki zuba aciki sannan saiki dora kan wuta ya dahu sosai sai ki sauke ki matse rake ki cire sannan ki tace ruwan bayan kin tace sai kuma ki maida kan wuta ki saka mazarkwaila a ciki sai ta narke sannan ki sauke kisa a fridge yayi sanyi sai kisha lokacin shan ruwa, wannan hadin tsumin manyan mata sun dade suna amfani dashi kuma sun tabbatar da ni’imar da yake kara musu sannan yana gyara musu jiki sosai.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*