
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
A sakamakon ciye-ciyenmu na yau da kullum, a ci wannan a sha wancen, hakora sukanyi datti koh baya ga samuwar wasu kwayoyin cuta wato (bacteria) dake zama a cikin yawun baki, wasu masu ru6arda hakora ne, su kan janyo wasu cututtuka a cikin baki wato (oral infections) saboda taruwar kazanta a cikin baki.
Haka kuma zaku tarar da baki na wari, ta yanda magana a cikin jama’a zai maka wahala koh kuma sumbatar matarka koh mijinki zai zamo wani abin kyama a gareku baki daya.
Toh idan ka koh kuma kin tsinci kanki da wannan matsalar ga hanya ingantacce kuma mafi sauki da zaku bi ku tsabtace bakinku da hakoranku, bakinku zai daina wari sannan kuma hakoranku zasu yi haske suyita kyalli.
Zaku nemi garin citta karamin cokali daya da (baking powder wacce masu yin bread suke amfani dashi) rabin cokali ka gauraya sai ka matse lemun tsami daya a ciki sai ka saka a brush ka goge hakoranka da kyau sannan ka kurkure bakinka da ruwa ka zubar, toh kdan ka sake yin haka zaka ga hakoranka sun yi haske haka kuma bakinka zai daina wari, hakoranka zasu yi karfi sosai.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply