Kadan Daga Cikin Amfanin Hulba Ga Mata Wajen Kauda Kuraje, Gyaran Gashi Hadida Cikowar Gaba Da Cututtukan Farji

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Wannan rana zan kawo muku bayani ne dangane da amfanin Hulba ga lafiyar Dan Adam, hulba kamar yanda kuka sani, kalma ce ta larabci, da harshen turanci kuwa ana kiran ta da ‘Fenugreek’. Ita hulba wani tsiro ne mai matukar amfani ga lafiya, kuma shekaru aru-aru da su ka wuce al’umma suke amfani da ita don samun waraka daga wasu cututtuka.

Jama’a da dama suna amfani da ganye da kuma kwayar hulba wajen samar da magunguna tun a shekarun da suka wuce, Hulba ta shahara a kasashe da dama a duniya, sai dai anfi samun ta a wasu daga cikin kasashen Larabawa musamman kasar Misra, sannan ana samun hulba a kasar Sin da kuma kasar Indiya.

A kasar Indiya suna kiran ta da, ‘Methi’ a yaren Hindu, a yaren Telugu na Indiyan kuma suna kiran ta da ‘Menthulu’. Wani bincike da wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa, ya nuna cewa, Hulba ta shahara a kasar Indiya saboda amfaninta ga lafiya, ta yanda zaka iya kiran ta gidan kowa da akwaita.

A al’adance, mutanen kasar Indiya na amfani da kwayar hulba a matsayin wani mahaɗin samar da magunguna, bayan amfani dasuke da hulba don samar da wasu hade-hade na inganta lafiyar jiki, da kuma yanda suke amfani da hulba don kula da lafiyar gashin kai.

Sai dai kuma, binciken zamani na kwanan nan da masana suka gudanar a kan hulba ya nuna cewa, zata iya samar da magunguna da hade-haden inganta lafiya daga hulba, fiye da yanda jama’a suka sani a baya, daga cikin amfanin hulba ga lafiya da masanan su ka gano, har da taimaka wa ma su ciwon siga, ciwon ido, gyaran gashi da fata, hakanan kuma ana amfani da hulba kan matsalar basir, matsalolin ciki da sauran su.

Ka Kadan Daga Cikin Amfaninsa Da Kuma Yanda Akeyin Amfani Dashi:

  1. Hulba na hana Bushewar fata; Bincike ya tabbatar da cewa, yin amfani da hulba na hana bushewar fata. Saboda haka duk mai fama da wannan matsala ta bushewar fata zai iya amfani da hulba don maganin wannan matsala.

Yadda za’a yi amfani dashi kuwa shine, a samu garin hulba, a kwaba ta da ruwa, amma kwaben ya yi kauri, sai a shafa a fuskarsa, a barshi tsawon rabin sa’a, daga bisani a wanke.

  1. Hulba na maganin Basir; Ga mutanen da ke fama da wannan matsala ta basir, za su iya amfani da hulba su samu sauki cikin yardar Ubangiji. Za a samu hulba a dafa, sai a sauke, idan ta huce sai a zuba zuma, ake sha, musamman awa guda kafin a kwanta barci.
  2. Hulba na maganin rashin ruwan nono ga mai shayarwa; A wasu lokutan, akan samu mace ta haihu amma sai ta samu karancin nono. Yin amfani da hulba zai samarwa da mai shayarwa ruwan nono, kuma zai taimaka wajen girman jaririnta.

A kasashen dake nahiyar Asia, mata kan yi amfani da hulba don maganin matsalar rashin ruwan nono ga mai shayarwa. Masana sun ce, hulba na taimakawa wajen samar da ruwan nono ga mata ma su shayarwa ne, sakamakon wani sanadari mai suna ‘phytoestrogen’ da ta ke kunshe da shi. Ana samun wannan fa’ida ta hulba ne, ta hanyar shan ta cikin ruwan shayi.

Koh kuma, mace ta samu ‘ya’yan hulba ta dafa da man Ridi ta dinga ci har tsawon kwana 3, sannan ta rinka shafa man hulbar a nononta, In shaa Allah za’a samu biyan bukata. Domin kuwa za ta samu ruwan nonon da zai wadatar da jaririnta, kuma ya kasance cikin wadataccen lafiya da yardar Allah.

  1. Yin amfani da hulba na rage ‘kwalastaral’ wato (kitsen marar kyau) a cikin jini; Bincike ya tabbatar da cewa, yawan amfani da hulba na taimakawa wajen rage yawan kwalastaral a cikin jini, musamman marar amfani da ake kira ‘bad’ cholesterol koh kuma (LDL) da turanci.
  2. Sannan kuma ana amfani da hulba wajen maganin cushewar ciki; Hulba na taimakawa wajen saurin narkewar abinci, sakamakon haka sai ta ke maganin cushewar ciki. Duk ma su fama da matsalar cushewar ciki koh kuma kumburin ciki sakamakon rashin narkewar abinci sai ya dimanci amfani da hulba, zai samu sauki, in shaa Allah.
  3. Mata da dam suna amfani da hulba don karin ni’ima; Idan mace na fama da rashin ni’ima ko bushewar farji, za ta iya samun hulba ta yi amfani da ita, kuma insha Allahu za ta dace. Yadda za ta yi amfani da hulba don karin Ni’ima shine, ta samu ‘ya’yan hulba da kanumfari da ‘ya’yan Habbatusswaudah da kuma Zumarta mai kyau.

Za ta hada ‘ya’yan hulba da na Habbatusswaudah da kanimfari guri daya ta dafa su, idan sun dafu sai ta sauke ta jira ya huce, sannan sai ta zuba zumarta a ciki, ta dinga sha. Toh In shaa Allahu zatasha mamaki.

  1. Hulba na taimakawa wajen rage kiba/teba; Kamar yadda mu ka ambata a sama, mutanen nahiyar Asia, na amfani da hulba kan matsalolin lafiya da yawa, to, game da matsalar kiba ma,su kan yi amfani da hulba don su samu waraka. Yadda su ke yi kuwa shine, yawan sanya ta cikin cimakarsu.
  2. Yin amfani da Hulba na kara inganta lafiyar koda; Masana sun tabbatar da cewa, yawan yin amfani da hulba cikin abinci na kara inganta lafiyar koda, ta hanyar sabunta kwayoyin halittar kodar, da hana su lalacewa.
  3. Hulba tana taimakawa wajen sha’awar cin abinci; Ana amfani da hulba wajen magance matsalar rashin cin abinci. Idan mutum na fama da rashin sha’awar cin abinci, sai ya samu man hulba ya hada da zuma ya ke shan babban cokali biyu sau 3 a rana.
  4. Ana amfani da hulba don karin kiba; Wannan ba zai zo wa mai karatu da mamaki ba, idan ya yi la’akari da yadda mu ka bayyana a sama cewa, hulbar na taimakawa wajen sha’awar cin abinci, mun san kuwa cin abinci na da kyakkyawar alaka da samun kibar jiki. Saboda haka, mutanen da ke fama da matsalar rama, sakamakon murmurewa daga wata rashin lafiya za su iya amfani da hulba don samu waraka. Kuma za su iya amfani da hadin da mu ka fada a sama, kan karin cin abinci don wannan fa’ida.

Sai dai, wani tsokaci anan shine, mai son yin amfani da hulba don karin kiba, akwai bukatar bayan amfani da hulbar ya hada da cin abinci mai Gina jiki, kamar wake da dankalin turawa da kifi da sauran su, don kuwa hausawa na cewa, koh da kana da kyau toh ka kara da wanka, kuma koh ba komai wadannan dangin abincin zasu taimaka wajen kara wa jikinka karfi. Bayan haka kuma sai ka guji cin nau’ikan abinci ma su maiko sosai.

  1. Hulba na rage hadarin kamuwa da ciwon daji; Ba shakka hulba na rage hadarin kamuwa da ciwon dajin mama, musamman ga mata ma su shayarwa. Bincike ya nuna cewa, matukar mace mai shayarwa ta juri yin amfani da hulba, baya ga kara ma ta lafiya tare da jaririnta, hulba na ba ta kariyar kamuwa daga ciwon dajin mama (Breast cancer).
  2. Ana amfani da hulba don maganin ciwon tari da mura da kuma sauran ciwon sanyi da kan shafi makogwaron mutum.
  3. Hulba na taimakawa wajen samun lafiyar ciki, ta hanyar maganin matsalolin ciki.
  4. Mata na iya yin amfani da hulba don daidaita jinin al’ada ga matan da jinin ke mu su wasa.
  5. Ana amfani da hulba don maganin kaikayin gaba; Yadda za a yi shine, A samu hulba a hada da gishiri a dafa sannan a jira ya huce yadda ba zai yi lahani ga jiki ba, sai a zauna a ciki, zuwa wani lokaci, a kalla dai a samu minti 30 a cikin wannan ruwan hulba. Haka za a yi har a samu waraka. Idan kina bukata za ki iya hada shayin hulbar ki na sha, ko kuma bayan kin dafa da gishirin, bayan kin debi ruwan da za ki zauna sai ki rage wani, ki jefa tsamiya ki sha.
  6. Hulba na taimakawa mata dake fama da bushewar gaba; Ga matan dake fama da matsalar bushewar gaba, sai su samu man ridi su ke zubawa a cikin ruwan dumi su ke zauna wa a ciki, sannan daga bisani sai su ke yin matsi da Hulba, insha Allahu za a dace.
  7. Hulba na maganin ciwon ciki bayan mace ta haihu.
  8. Ana amfani da hulba domin gyaran nono; Bincike ya tabbatar da cewa ana amfani da hulba don gyaran nono, dalili kuwa shine, hulba na sanya fata da tsokar dake kewayen nonon mace su buɗe, hakan sai ya sa nonon ya ciko ɓulɓul abin sha’wa, musamman idan nonon ya kasance da girmansa amma ya kwanta.

Abubuwan da ake bukata kuwa sune; garin hulba da garin Shammar da kuma zuma.

Yanda Za’a Hada Kuwa:

Dafarko za’a samu garin hulba da garin shammar, za’a ɗiba cikin ƙaramin cokalin guda 1 na garin hulba sai a zuba a cikin kofi mai tsafta da aka tanada, sannan a zuba garin shammar din shima cikin ƙaramin cokali guda, sai a gauraye su waje daya, daga bisani a dafa ruwa idan ya tafasa sai a kwara a kan garin hulba dana shammar dake cikin kofin a juya su da cokali, bayan haka sai a rufe kofin. Bayan kamar minti Goma sai a tace da rariya, bayan an tace, sai a kawo zuma mai kyau a zuba a rinka Sha.

Daga Nan kuma sai a shafa man hulba a nonon, amma wajen shafawa akan nonon a tabbatar an murza man hulbar sosai akan nonon gaba daya yanda zai shiga fatar nonon da kyau. Za’a sha wannan hadin sau 2 a rana, da safe da kuma dare, kuma duk lokacin da aka kammala shan shayin hakanan za’a shafa man hulbar a kan nonon, shi ma ya zama sau biyu kenan.

Ta yanda zaki gane maganin na amfani shine, ta hanyar jin nononki na kara nauyi, alamar ya fara cikowa kenan Allah yasa mu dace.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*