‘Yar Uwa Shin Kinsan Sirrin Dake Tattare Da Jigida A Kugun Mata:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng

Ita dai jigida kamar yanda akafi saninta a hausance wata damarace da mata suke daurawa akan kugunsu.

Sannan kuma ita dai jidiga a tun dori anayinsa ne da dutse na sakiya ga masu hali, su kuma talakawa ana musu nasu jigidan ne da wani roba mai dauke da launuka daban-daban domin karawa abun kyau da armashi a idanuwan masu kallo.

Sannan larabawa da indiyawa sune sukafi amfani da jigida tun fil azal kamar yanda bincke ya nuna, hakan kuwa baya rasa nasaba da yanayin yanda suke rawan al’adarsu idan suka kada da kuma girgiza kugunsu jigida na aman sauti yana hawa yana sauka, Abin nufi zakuji yana Kara.

Sai dai kuma a baya kabilu da damar gaske na Africa suna amfani da jigida sosai fiye da yanda larabawan da Indiyawan suke yi ganin yanda su bakaken Fata na Afirka suka maida jigida cikin wasu jerin al’adunsu da kuma camfe-camfe irin nasu.

Wasu daga camfin da akayiwa Jigida a nahiyar Afirka shine, yana taimakawa mata masu ciki sauki wajen haihuwa, haka nan kuma budurwar da take sanya jigida tafi saurin sa’ar aure da wuri. Hakan kuma duk macen dake sanya jigida aljanu koh kuma wasu abubuwa na sammu bazai kamata ba. A camfi na wasu kabilun na Afirka kenan.

Shi dai jigida irin na da ba haka kawai ake sakashi ba, domin shahararru kuma jarumai ne a wacan lokacin suke yinta don haka ne take da tasiri da kuma tsada ga masu sayensa.

Sai dai a baya akwai jigida na ‘yan mata sannan kuma akwai na Matan aure da kuma na tsoffofi, kuma a wannan lokacin babu matsala koh kuma wani gani-gani da ake yiwa macen da aka ganta sanye da jigida saboda abune da aka dauka na al’ada a maimakon ado koh kiran maza da wasu ke ganin matan yanzu suke yi da jigida ba gaskiya.

Yanzu dai sanya jigida ga mata ya bunkasa ya fadada har cikin turai. Matan turawa kamar yanda bincike ya tabbatar da kashi sittin cikin dari suna saka jigida.

Sai dai a wannan zamanin da muke ciki sanya jigida ga mata ya zama abun ado ne ba domin dalilai irin na canfi da muka ambata a baya da mutanen da suke yi ba, duk da yake ana samun kadan daga cikin mata kauyawa masu saka jigida da manufa na canfi.
Shima dai kamar irin na da ne, wannan zamanin ana yin jigida ne da wasu duwatsu masu kyalli da kuma robobi masu sheki wadanda nauyinsu bai kai irin na zamanin baya ba.

Toh amma babban alfanun da jigida yake yiwa mata kamar yanda bincike ya tabbatar a wannan lokacin shine, yana karawa mace fadin kugunta ga irin matan nan da suke da karancishi.

Akwai maza da dama da aka zanta dasu Kuma sun nuna sha’awarsu na ganin matansu na aure suna saka jigida domin yana karamusu kyau musamman idan mace tana sanye da kayan da zasu bayyana mata su, har illa yau cikin alfanun da jigida yake dashi shine yakan motsa sha’awan maza a yayin da suka ji sautinsa ko suka hango shatinsa.
Kararsa koh sautin dake fitowa daga jigida a lokacin wasannin motsa sha’awa da kuma lokacin gudanar da yin jima’i abune dake himmanta maza kuma yake kara musu kuzari da azama hadida himma.

Amma kuma duk da wadannan tasiri, mahimanci da alfanun da jigida yake dasu ba duka mata bane suke sanyawa ba, haka ma maza da dama basu son ganin mace da jigida a kugunta wasu mutane sun riga sun kudura cewa duk mace koh budurwar da aka ga tana sa jigida koh akaji karar sautinsa a tare da ita suna daukan irin wa’innan matan mazinata ne wanda Kuma Sam ba haka bane, saidai kuma Akwai ina akwai na Allah sannan kuma akwai na banza.

Shan koko daukan rai ne, sannan kuma bincin wani gubar wani, wannan shine.

Amfani Da Muhimmancin Jigida A Kugun Mata:

Shin Mema Ake Nufi DaJigidar Ita Kanta:

Toh kamar dai yanda nayi muku bayani a baya, ita dai jigida wata sarka ce wacce mata suka fi amfani da ita musamman daga arewacin kasa duk kuwa da cewar akwai abun da mutanen da suke yiwa lakabi da birjani, toh shakka babu ya danganta da yanayin al’adar mutane amma Maza koh mata suna yin amfani da shi.

”PTH” tace Bisa ga al’adun gargajiya mutanen Afrika na bayan kwaliya akwai wasu dalilai da yasa suke saka jigida musamman ma matan su.

  1. A wasu yankunan ana hada jigidan mata su saka domin samun kariya daga iska koh mutanen boye wato jinnu
  2. Sannan kuma wani jigidan akan haɗa da surkulle ne domin wai ya kare mace daga kamuwa da cututtuka musamman kananan yara amma kuma har manyanma sunayi.
  3. Wasu jigidan akan haɗa su mace ta saka a kwankwaso domin samun saukin naƙuda a lokaci haihuwarta.
  4. Kuma akwai masu yakinin cewa saka Jigida na taimakawa wajen rage kiba musamman ga mata masu tumbi koh kuma katon ciki.
  5. Haka zalika kuma jigida na taimakawa wa mace wajen ƙara girman kugu wato Hips a Turance, dakuma samun farin jini cikin mutane
  6. Jigida na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo sha’awa da ra’ayin namiji zuwa ga mace zakiga wata macen data wuce sai namiji yabita saboda karar wannan jigida.

Amma kuma duk da wa’innan kyawawan dalilan wasu daga cikin mutane da dama basu son jigida saboda a ra’ayinsu jigida sarka ne da ake amfani da shi domin wani tsafi koh shirka.

Wata mata da ta shahara a hada jigida Felicia Musa ta ce tana matukar sha’awar jigida musamman idan mace ta saka shi yana kara idan tana tafiya ma haka zakaji yana Bada sauti.

Ta Kara da cewa jigida iri-iri ce akwai wanda wasu matan suke sakawa na farin jini koh na samun kariya amma yin hakan ba shine ke mai da mutum matsafi ba gaskiya.

Felicia ta ce saka jigida ra’ayi ne idan kana so ka saka idan kuma ba ka so ba za ka saka ba amma rashin son shi din ba shine zai bawa mutum daman cusa wa mutane ra’ayin kin shi koh kuma rashin son shi ba.

Daga karshe Jigida tana tayarwa wasu Mazan da shaawa, sau tari wani Namijin sha’awar sa tana dagawane idan yaji mostin Jigida wato karar.sautinshi.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Groups

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*