Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na starsbio.com.ng
Shi farin wake yana dauke da wadataccen sinadarin calcium wanda yake da matukar amfani wajan karawa kasusuwa da hakora wato haure karfi, ana son mace mai ciki ta rinka cin farin wake musamman ma wasu suna sarrafa shi ta hanyoyi da dama kamarsu faten wake, Alale wato (moi-moi), adafa wake da shinkafa koh a dafa shi haka kawai ba tare da anyi fatenshi ba acishi shi kadai ba tare da wani hadi ba, toh lallaikam duk mai cikin da ta dauki wake a matsayin abincin da takeci a kusan kullum lallai za kuga lafiyarta da ta jaririnta sunyi daban da wacce ba ita ba a lokacin da take da ciki da kuma bayan ta haife cikin nata.
Sannan kuma bayan cin farin wake akwai abubuwan da suke ɗauke da sinadarin calcium da kuma wadanda abubuwa da shawarwarin da ake son mace mai ciki koh mai shayarwa koh kananan yara su rinka amfani da su akai-akai sune gasu kamar haka:
- Shan Madara koh Nono
- A rinka cin dafaffen Kwai
- Kubewa (a rinka shan miyan kubewa akai-akai danye koh busasshiya).
- Sai a rinka shafawa kananan yara nan zaituun a ƙafafuwan su saboda hakan yana sanya kafarsu tayi kwari sosai har su fara iya yin tafiya da wuri da izinin Allah.
- San an a rinka shafawa jariri man tafarnuwa mai kyau a dasashinsa saboda rigakafin ciwon fitowar hakori da kuma rage radadin da yara sukeji wajen fitowar haƙoran, kuma zazzabin nan na fitowar hakori da yawan kashi, yaro zai rage yinsu sakamakon amfani da wannan tsarin da ikon Allah.
- Mai ciki idan ya kai wata bakwai toh tarinka dafa ‘ya’yan hulba, da ‘ya’yan Habbatusswaudah da kuma ganyen na’a-na’a koh kuma ganyen Doddoya tana sha da safe da dare har lokacin da zata haihu, Wannan yana matuƙar taimakawa mai ciki sosai kuma yana taimakawa jaririnta ya samu kuzari da kwarin jiki, lafiyar jiki da kuma Basira zaiyi daban da sauran yaran da ba ayi musu wannan tsarin ba in shaa Allah.
- Idan kuma mace ta haihu ana so ta rinka amfani da abubuwan can da na lissafo a farko, da kuma dafa wadan nan, kaninfari, citta da kuma lipton.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
Leave a Reply